Home Back

Aiki da Cikawa: Ana Tsaka da Bikin Babbar Sallah, Sojoji Sun Kashe Dan Bindigan da Ya Addabi Kaduna

legit.ng 2024/7/6
  • Sojoji a jihar Kaduna sun yi nasarar hallaka wani kasurgumin dan ta’adda mai alaka da Buharin Yadi a ranar Sallah
  • Rahoto ya bayyana kayayyakin da aka kwato a tattare da kasurgumin dan ta’addan da aka kasha a karamar hukumar Giwa
  • Sojojin Najeriya sun bayyana aniyarsu na tabbatar da ci gaba da wanzar da zaman lafiya a yankuna daban-daban na kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Kaduna - Bayan kusan mako guda da kashe daya daga cikin kasurguman ‘yan ta’adda a Arewa maso Yamma, Buharin Yadi, da dakarun 1 Division suka yi, sojoji sun ga bayan daya daga cikin abokan barnarsa, Daushe.

An sheke Daushe ne a ranar babbar sallah, Lahadi, 16 ga Yuni, lokacin da sojoji suka kaddamar da farmaki kan ‘yan ta’adda a karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

An hallaka shugaban 'yan bindiga a Kaduna
Yadda aka kashe kasurgumin dan bindiga a jihar Kaduna Asali: Original

Domin cimma nasarar aikinsu na tabbatar da tsaro, an tura undunar sojoji zuwa yankin Sabon Layi, inda suka kutsa har yankin Kidandan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji na aikin tabbatar da tsaro a bikin sallah

Yayin da suka kusanci Kidandan, sojojin suka hango dan ta'addan yana tuka babur dinsa da gudu a kokarinsa na tserewa daga idon sojojin, kamar yadda kafar labarai ta Zagazola Makama ta ruwaito.

Nan take sojoji suka bi shi a guje har ta kai gay a jefar da babur din ya shilla a guje zuwa wani yankin da sojoji suka tarfa shi suka sheke.

A halin da ake ciki, sojoji na ci gaba da aiki don tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a jihohin Najeriya yayin da ake ci gaba da bikin sallah.

‘Yan bindiga sun yi ta’asa a jihar Sokoto

A wani labarin, rahotannin da ke fitowa na cewa da safiyar Lahadi, 16 ga Yuni, wasu 'yan bindiga sun kai hari wani kauye a jihar Sokoto.

An rahoto cewa, tsagerun sun kashe mutane da yawa kuma sun sace wasu a lokacin wannan harin.

An samu labarin cewa maharam sun farmaki kauyen Dudun Doki a karamar hukumar Gwadabawa ta jihar Sakkwato, inda suka kashe mutane fiye da goma kuma suka sace mutane da yawa a wajen karfe 1.30 na dare, rahoton Vanguard.

Asali: Legit.ng

People are also reading