Home Back

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka A Fannin Kimiyya Da Fasaha Zai Taimakawa Afirka Wajen Samun Ci Gaba

leadership.ng 2024/7/5
Hadin Gwiwar Sin Da Afirka A Fannin Kimiyya Da Fasaha Zai Taimakawa Afirka Wajen Samun Ci Gaba

Gwamnatin kasar Sin ta gudanar da babban taron karrama masu nazarin kimiyya da fasaha a jiya, inda aka samar da dimbin kyaututuka ga fitattun ma’aikata masu nazarin kimiyya da fasaha na kasar, don yaba musu bisa muhimmiyar gudunmowar da suka samar a fannin nazari kan bangarori masu alaka da kimiyyar lissafi ta Physics, da aikin safiyo ta tauraron dan Adam mai hango abubuwan dake doron kasa, da sinadaran da ake amfani da su wajen hada kayayyakin latironi, gami da aikin gona, da dai sauransu. Mai bayar da kyautuka a wajen taron shi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, lamarin da ya nuna matukar muhimmancin da kasar Sin ta dora ma kimiyya da fasaha, da bangaren kirkire-kirkire. To, sai dai wane irin tasiri ci gaban kasar Sin ta fuskar kimiyya da fasaha zai samar wa kasashen Afirka?

Dangane da wannan tambaya, su ‘yan Afirka suke da ikon ba da amsa. Olusegun Oyebade Ikusika, wani shehun malami ne dake aiki a jami’ar Fort Hare ta kasar Afirka ta Kudu, wanda ke mai da hankali kan nazarin hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin ta fuskar kimiyya da fasaha, cikin shekarun nan. Yayin da yake hira da manema labaru na kasar Sin a kwanan baya, ya ce, ilimi da fasahohi na kasar Sin, da hadin gwiwar Afirka da Sin a fannin kimiyya da fasaha, suna taka muhimmiyar rawa wajen taimakon kasashen Afirka tinkarar manyan kalubaloli, musamman ma a fannonin aikin jinya da kiwon lafiya, da tabbatar da samar da isashen abinci, da dai sauransu.

Furfesa Ikusika ya ambaci taimakon da kasar Sin ta ba kasashen Afirka, a kokarinsu na tinkarar annoba da cututtuka. Misali, bayan da aka samu barkewar annobar cutar Ebola a yankin yammacin Afirka a shekarar 2014, nan take kasar Sin ta tura kwararrun ma’aikata masu ilimin aikin likitanci zuwa wuraren da annobar ta shafa, inda suka yi aiki kafada da kafada da likitocin kasashen Afirka. An ce, ya zuwa shekarar 2015, an riga an tura kwararrun likitocin kasar Sin 102, cikin jeri 13, zuwa kasashen Afirka, inda suka ba da taimako kan kokarin yakar cutar Ebola, bisa ilimi da fasahohin da suka mallaka ta fuskar aikin likitanci. Sa’an nan, bayan da annobar cutar COVID-19 ta barke, kasar Sin ta ba da tallafin ginin hedkwatar cibiyar kandagarkin yaduwar cututtuka ta kungiyar kasashen Afirka (AU), wanda shi ma ya kansance alamar hadin gwiwar da Afirka da Sin suke yi ta fuskar kimiyya da fasaha masu alaka da aikin likitanci da kiwon lafiya.

Ban da haka, Farfesa Ikusika ya ambaci hadin kan kasashen Afirka da kasar Sin a fannin aikin gona, inda a wannan bangare, ya ba da misalin kasar Madagascar. A cewarsa, kasar ta dade tana fama da matsalar koma bayan fasaharta ta noman shinkafa. Ganin haka ya sa kasar fara hadin gwiwa da kasar Sin a shekarar 2007, inda ma’aikata masu fasahohi na kasar Sin suka fara yayata fasahar noman shinkafar da aka tagwaita irinta a kasar ta Madagascar, ta yadda yawan shinkafar da a kan girba a kasar ya karu zuwa ton 7.5 kan gona mai kadada guda. Zuwa yanzu, kasar tana kan gaba a tsakanin kasashen Afirka, a fannonin yawan noman shinkafar da aka tagwaita irinta, da yawan shinkafar da aka samar. Haka zalika, ita ce kasar Afirka daya tilo, wadda ta mallaki cikakken tsarin masana’atu mai alaka da shinkafar da aka tagwaita irinta, wanda ya kunshi bangarorin samar da iri, da noman shinkafa, da sarrafa ta, gami da sayar da kayayyakin abinci da aka hada da shinkafar.

Sa’an nan bisa matsayinsa na mai nazarin kimiyya da fasaha na kasar Afirka ta Kudu, Olusegun Ikusika ya ambaci wani bikin da gidan jakadancin Sin dake kasar Afirka ta Kudu ya gudanar, wanda ya ba matasan kasar damar hira tare da ‘yan saman jannatin kasar Sin dake cikin tashar binciken sararin samaniya ta kasar. A cewarsa, wannan biki ya ba kasashen Afirka ta Kudu da Sin damar kara fahimtar juna a bangaren kimiyya da fasaha, da janyo hankalin karin matasan kasar Afirka ta Kudu ga fasahohi masu alaka da zirga-zirgar kumbuna a sararin samaniya.

Sai dai kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya sun saba da shafa bakin fenti kan duk wani hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Misali, sun ce wai hadin kan Sin da Afirka ta fuskar kimiyya da fasaha ya nuna alamar “sabon nau’in mulkin mallaka”. Dangane da zancen, Farfesa Ikusika ya musanta cewa, ba a taba saka wani sharadi kan hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin kimiyya da fasaha ba, kana wannan huldar hadin kai ta amfani kasashen Afirka, a kokarinsu na kawar da talauci, da neman samun ci gaban tattalin arziki. Alal misali, fasahar kasar Sin ta noman laimar kwado, wadda aka fi san ta da fasahar Juncao, ta riga ta zame wa dimbin manoman kasashen Afirka wata muhimmiyar dabarar samun wadata.

Hakika, duk mutumin da ya shaida yadda ma’aikata masu nazarin kimiyya da fasaha na kasar Sin suke gudanar da ayyukansu a nahiyar Afirka, to, ba zai taba nuna shakku kan sahihancinsu ba. Misali, a kasar Kenya, Farfesa Xiong Youcai da abokan aikinsa na jami’ar Lanzhou ta kasar Sin sun shiga kauyukan kasar har sau 30 cikin shekaru 12 da suka gabata, don yada fasahar noman masara mai tsimin ruwa ta hanyar amfani da wani nau’in leda na musamman wajen rufe gonaki, wadda ta sa aka samu karuwar masara da ta kai kashi 99% zuwa 240%. Wesly Kiprotich, wani matashi dan kasar Kenya ne dake bin Farfesa Xiong domin koyon ilimin aikin gona, a cewarsa, “Manoman kasarmu su kan kammala aiki da kimanin karfe 2 da wani abu da rana, amma Farfesa Xiong da abokan aikinsa su kan fara aiki da karfe 8 na safe, kuma ba sa gama aiki sai zuwa karfe 6 na maraice. Mutane suna mamaki, suna cewa kamar ba su san gajiya ba. ”

To, mene ne abun da Farfesa Xiong yake nema? A cewarsa, kawai yana neman ganin wata fasahar noma mai farin jini a kasar Sin, ta ci gaba da taka rawar gani a fannin ingiza aikin gona, bayan kai ta nahiyar Afirka. Wannan yunkuri na son ganin ci gaban harkoki a kasashen Afirka, ya zo daga tunanin Sinawa na “Al’ummar dan Adam mai makomar bai daya”. A ganin mutanen Sin, ya kamata dukkan mutanen duniya su samu damar jin dadin rayuwa, ta hakan ne za a iya tabbatar da zaman lafiya da ci gaban al’ummar dan Adam mai dorewa, a duniyarmu.

To, bisa wannan tunani mai muhimmanci, za mu san cewa, tabbas hadin gwiwar Sin da Afirka ta fuskar kimiyya da fasaha za ta ci gaba da amfanawa kokarin kasashen Afirka na raya tattalin arziki. (Bello Wang)

People are also reading