Kotu ta yi Fatali da Karar da Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu ya Shigar kan Gwamnati
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja- Babbar kotu da ke zamanta a Abuja ta yanke hukunci kan karar da daurarren shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ya shigar gabanta.
Nnamdi Kanu, ta bakin lauyoyinsa ya shigar da gwamnatin tarayya da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) kotu ya na neman a biya shi diyyar N1bn.
Nigerian Tribune ta tatatro cewa mai shari'a, James Omotosho a yau ya yi fatali da karar ta Nnamdi Kanu saboda gaza nunawa kotu bukatar haka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai shari'a James Omotosho ya kori karar da Nnamdi Kanu ya shigar ya na kalubalantar hukumar DSS da yi masu kutse da sauraron bayanai tsakaninsa da lauyoyinsa a sirrance.
Jaridar Punch ta wallafa cewa da ya ke yanke hukuncin, alkalin ya bayyana cewa Mista Kanu ya gaza kawo hujjojin da za su tabbatar da zarge-zargen da ya yi.
Haka kuma mai shari'a Omotosho ya jaddada cewa lauyoyin Kanu sun gaza tabbatar da hujjojinsu na zargin kin yi masu adalci a shari'ar da ake gudanarwa.
A wani labarin kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta ki bayar da belin shugaban haramtacciyar kungiyar ta IPOB, Nnamdi Kanu.
Haka kuma mai shari'a Binta Nyako ta nemi a gaggauta ci gaba da shari'ar da ake yi tsakaninsa da gwamnatin Najeriya kan cin amanar kasa da tayar da zaune tsaye.
Asali: Legit.ng