Home Back

Gwamnati Ta Ceto Sauran Daliban Jami’a da Aka Sace Bayan Miyagu Sun Hallaka 2

legit.ng 2024/7/9

Gwamnatin jihar Kogi ta sanar da ceto dalibai takwas daga cikin 32 da aka sace a jihar a farkon watan Mayu da ta gabata

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi – Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da ceto sauran daliban Jami’ar CUSTECH da aka sace a jihar.

Ceto daliban guda takwas da aka yi yanzu ya tabbatar da kwato mutane 30 kenan daga hannun ‘yan bindiga.

Wannan na zuwa ne bayan sace dalibai guda 32 da maharan suka yi a farkon watan Mayu yayin da suka hallaka biyu daga ciki, cewar Punch.

Kwamishinan yada labaran jihar, Kingsley Fanwo shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa a yau Lahadi 2 ga watan Yuni.

Kungsley ya ce gwamnan jihar, Usman Ododo ya ba da umarnin ba da duka gudunmawa domin hada daliban da iyayensu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karin bayani na tafe…

Asali: Legit.ng

People are also reading