Back to the last page

Man City za ta saki Grealish domin Bellingham, Arsenal na son Asensio, Utd na son Zubimendi

bbc.com 11 hours ago

Asalin hoton, Getty Images

Manchester City za ta iya sayar da dan wasanta mafi tsada Jack Grealish, domin ta samu kudin sayen dan uwansa dan Ingila Jude Bellingham, mai shekara 19, daga Borussia Dortmund. 

Ita ma kungiyar Paris St-Germain tana son matashin dan wasan na tsakiya Bellingham. 

Arsenal na sha’awar sayen Marco Asensio na Real Madrid, dan Sifaniya a watan Janairu.

Har yanzu Cristiano Ronaldo bai yanke shawara ba a kan ko ya karbi tayin da kungiyar Al-Nassr ta Saudiyya ta yi masa na biyansa albashin fam miliyan 173 a shekara ba.

Tsohon dan gaban na Manchester United zai bayyana matsayarsa ne bayan gasar Kofin Duniya.

Sha’awar da Tottenham da Chelsea ke yi kan dan bayan RB Leipzig na Croatia Josko Gvardiol, mai shekara 20, na karuwa kafin lokacin kasuwar ‘yan wasa ta Janairu. 

Idan har Barcelona ba ta yi magana kan sayen dan bayan Borussia Dortmund ba Thomas Meunier, dan wasan na Belgium zai saurari bukatar wasu kungiyoyin da suka hada da AC Milan da Juventus da Manchester United da kuma wasu kungiyoyin London biyu. 

Shi kuwa dan wasan gaba na gefe na Atletico Madrid, Matheus Cunha, na Brazil zai koma Wolves a watan Janairu.

Kociyan Leeds United Jesse Marsch ya ce saura kadan kungiyar ta sayi Cody Gakpo daga PSV Eindhoven a watan Agusta, kuma yanzu Manchester United na nuna sha’awarta ta sayen dan gaban na gefe na Netherlands a watan Janairu.

To amma shi kuwa Gakpo din bayan da ya taimaka wa kasarsa kai wa wasan dab da na kusa da karshe a gasar Kofin Duniya, ba ya tunanin kungiyar da zai tafi sai kamar yadda ya ce watakila bayan sun zama zakaru.

A shirye Manchester United take ta biya kudin sakin dan wasan tsakiya na Real Sociedad Martin Zubimendi, fam miliyan 51.4 domin daukar dan Sifaniyan.

Inter Milan na son daukar Romelu Lukaku, aro na karin shekara daya daga Chelsea.

Flamengo ta zuba ido tana lura da abin da ke faruwa game da dan gaban Tottenham Lucas Moura na Brazil bayan da tsohuwar kungiyarsa Sao Paulo ta kasa cimma yarjejeniya da shi.

Dan wasan tsakiya na Netherlands Frenkie de Jong ya tattauna da Manchester City da Paris St-Germain kafin daga karshe ya yanke shawarar tafiya Barcelona daga Ajax a 2019.

Shugaban PSG Nasser al-Khelaifi ba ya tunanin kungiyar za ta sayi sabbin ‘yan wasa a watan Janairu.

Leeds United na duba yuwuwar sake dawo da dan gabanta na gefe Chris Wood dan New Zealand a watan Janairu daga Newcastle United. Wood ya bar kungiyar ne ya tafi Burnley a 2017. 

Ana duba yuwuwar daukar tsohon kociyan Leeds Marcelo Bielsa domin ya maye gurbin Diego Alonso a matsayin kociyan Uruguay na gaba.

Back to the last page