Home Back

Jirgin Sojojin Saman Najeriya Ya Yi Hatsari, Matuƙin Jirgin Ya Sha da Kyar

legit.ng 3 days ago
  • Jirgin saman rundunar sojin saman Najeriya ya yi hatsari a wani ƙauye dake Igabi a jihar Kaduna
  • Cike da gwanancewa tare da kiyaye dokar saukar gaggawa, matuƙin jirgin ya sauka tare da tsira da ransa
  • Mazauna yankin sun hanzarta kai ɗauki bayan jin ƙarar faduwar jirgin, daga bisani sojoji suka mamaye wurin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Wani jirgin dakarun sojin saman Najeriya ya tafka hatsari a sa'o'in farko na ranar Litinin a ƙauyen Tani dake ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Wani ganau ba jiyau ba, wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa, ya ce lamarin ya faru ne wurin ƙarfe 5 na asuba, wanda ya haifar da tashin hankali ga mazauna yankin.

Jirgin sojojin Najeriya yayi hatsari
Kaduna: Jirgin NAF yayi hatsari, matukin ya fita. Asali: Facebook

Jigin sojojin Najeriya yayi hatsari

Daily Trust ta tattaro cewa, jirgin mai saukar ungulu, wanda ke sararin samamiya yana aiki ya fuskanci wata babbar matsala wanda ya kai ga hatsarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cike da sa'a, matuƙin jirgin yayi nasarar bin ladubban saukar gaggawa wanda hakan yasa ya tsira da ransa.

Tuni mazaua ƙauyen Tami suka garzaya wurin da hatsarin ya faru, inda suka bada taimakon gaggawa tare da nuna jin dadinsu saboda ba a yi rashin rai ko ɗaya ba.

Mazauna kauyen sun kai dauki

"Mun ji ƙarar faduwar wani abu, wanda ya sa muka garzaya wurin da lamarin ya faru.
Mun yi mamaki matuka tare da samun nutsuwa bayan da muka tarar matuƙin jirgin yana nan da ransa."

-Inji mazauna garin.

Sojoji sun dura wurin da jirgin ya sauka

Tawagar jami'an sojoji daga NAF sun hanzarta isa wurin tare da kewaye shi kuma sun fara binciken farko, jaridar Tribune Online ta ruwaito.

Sun kange wurin da hatsarin ya faru domin hana shigar waɗanda ba hukuma ba tare da tabbatar da kariyar mazauna ƙauyen.

Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, Rundunar Sojin Saman Najeriya, bata fitar da takarda a hukumance ba game da lamarin.

Asali: Legit.ng

People are also reading