Home Back

KARA DA KIYASHI: Amurka ta fara kwashe sojojin ta daga Nijar

premiumtimesng.com 2024/7/2
KARA DA KIYASHI: Amurka ta fara kwashe sojojin ta daga Nijar

Rundunar Sojojin Amurka da ke da Sansanoni a Afrika (AFRICOM), ta tabbatar da fara janye dakarun ta daga Jamhuriyar Nijar, da a karon farko ya kawo sauya kaka-gidan dakarun Amurka a yankin Sahel.

Gingimemen jirgin farko samfurin C-17 Globemaster III, ya bar Filin Saukar Jiragen Yaƙi na Yamai ranar 7 ga Yuni, ɗauke da sojojin Amurka.

Sama da shekaru goma kenan Jamhuriyar Nijar ke adawa da girke sojojin Amurka a ƙasar, wanda aka girke domin taimakawa wajen yaƙi da ta’addanci da kuma wanzar da zaman lafiya a yankin Sahel.

Wannan janyewa ta ƙara tabbatar da sauya alƙiblar shugabannin Jamhuriyar Nijar, waɗanda suka maida alƙiblar difilomasiyyar ƙasar ta karkata ga ƙasar Rasha, tare da juya wa Faransa da Amurka baya, tun bayan hamɓarar da tsohon Shugaban Ƙasa, Mohammed Bazoum, wanda sojoji suka maye gurbin sa da Janar Abdourahmane Tchiani, kusan shekara ɗaya da ta gabata kenan.

Mahukuntan Amurka sun ce ana janye sojojin tare da haɗin guiwar ƙasar Nijar, kuma za a kammala a ranar 15 ga Satumba, 2024.

People are also reading