Home Back

Darajar Naira Ta Ragu, Dalar Amurka Ta Ƙara Tsada a Kasuwa a Najeriya

legit.ng 2024/7/5
  • Farashin Dalar Amurka ya ƙaru a kasuwar hada-hadar musayar kuɗi ta gwmanati ranar Talata, 4 ga watan Yuni, 2024
  • Rahoton shafin hada-hadar kɗi FMDQ ya nuna Naira ta faɗi zuwa N1,476.95 kan kowace dala idan aka kwatanta da farashin ranar Litinin
  • Wannan dai na zuwa ne a lokacin da CBN ke ci gaba da ɗaukar matakai da nufin dawo da ƙimar Naira kan Dalar Amurka a ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kimar kudin Najeriya wanda muka fi sani da Naira ta ragu a kasuwar hada-hadar cinikayyar kuɗi ta gwamnati ranar Talata, 4 ga watan Yuni, 2024.

Dalar Amurka ta ƙara tsada, inda ta koma N1,476.95 kan kowace Dala guda a kasuwar gwamnati jiya.

Musaya daga Dala zuwa Naira.
Kimar Naira ta ɗan faɗi kaɗan a kasuwar hada-hada ta gwamnati a Najeriya Hoto: Contributor Asali: Getty Images

Bayanai daga shafin kula da hada-hadar musayar kuɗin waje FMDQ na ranar Talata ya nuna cewa ƙimar Naira ta ragu da Kobo 83.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Tribune Nigeria ta tattaro cewa hakan na nufin Naira ta faɗi da kaso 0.06% idan aka kwatanta da farashin N1,476.12/1$ da aka yiɓmusanya ranar Litinin.

Har ila yau, adadin kuɗin da aka yi cinikayyarsu ranar Talata ya ƙaru zuwa Dala miliyan 236.99 daga Dala miliyan 121.87 da aka yi hada-hada da su ranar Litinin.

Bugu da ƙari, a kasuwar masu zuba jari (I&E), an yi hada-hadar musanya kuɗin Najeriya a farashi tsakanin N1,500.00 da N1,362.15 kan kowace Dala.

Legit Hausa ta fahimci cewa a halin yanzun ƙimar Naira na faɗuwa wani lokacin kuma ta farfaɗo a kasuwar gwamnati da kasuwar bayan fage ta ƴan canji.

Wannan na zuwa ne duk da matakan da babban bankin Najeriya (CBN) ke ci gaba da ɗauka da nufin farfaɗo da darajar Naira.

Farashin Naira dai na da tasiri a rayuwar ƴan Najeriya ta yau da kullum bisa la'akari da yadda ake famada tsadar kayayyakin abinci da sauransu.

A wani rahoton kuma

Asali: Legit.ng

People are also reading