Home Back

Yin Watsi Da Babakere Da Daina Cin Riba Daga Yake-Yake Mafita Ce Ta Warware Matsalar ‘Yan Gudun Hijira A Duniya

leadership.ng 2024/7/1
Yin Watsi Da Babakere Da Daina Cin Riba Daga Yake-Yake Mafita Ce Ta Warware Matsalar ‘Yan Gudun Hijira A Duniya

Ran 20 ga watan nan da muke ciki, ta kasance ranar kare hakkin ‘yan gudun hijira ta duniya. Hukuma mai kula da harkokin ‘yan gudun hijira ta MDD ta ba da wani rahoto a kwanan baya cewa, ya zuwa karshen watan Mayu na bana, yawan ‘yan gudun hijira a duniya ya karu cikin shekaru 12 a jere, wanda har ya kai miliyan 120.

Rashin samun kwanciyar hankali da daidaiton ci gaba shi yake haifar da matsalar ‘yan gudun hijira. Daga Afghanistan zuwa Sham, ba a kawo karshen matsalar ba tukuna, ga shi rikicin jin kai da zirin Gaza ke fuskanta ya tsananta, inda yawan mutanen da suka rasu ya haura dubu 37, yayin da wasu fiye da dubu 85 suka raunata, sai kuma mutane fiye da miliyan 2 aka raba su da muhallinsu. Ya zama dole a tabbatar da tsagaita bude wuta da ingiza yin shawarwari nan da nan.

Sai dai da wuya a kai ga magance matsalar ‘yan gudun hijira yadda ya kamata, duba da cewa wasu kasashen yamma sun nace ga ra’ayin babakere da tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe ta hanyar nuna karfin tuwo da yunkurin cin riba daga yake-yake. Kamata ya yi wadannan kasashe sun dudduba matsalolinsu su kawar da wadannan ra’ayoyi sun sauke nauyin dake wuyansu na magance matsalar, tare da yin hadin gwiwa da duniya wajen kyautata tsarin kare ‘yan gudun hijira, ta yadda za a ingiza warware matsalar ‘yan gudun hijira daga tushe. (Mai zane da rubutu: MINA)

People are also reading