Home Back

Soke Naɗin Sanusi II: Gwamnatin Kano Ta Yi Martani Kan Hukuncin da Kotu Ta Yanke

legit.ng 2024/7/6
  • Gwamnatin jihar Kano ta ce hukuncin da babbar kotu ta yanke ya nuna cewa har yanzu Muhammadu Sanusi II ne Sarkin Kano
  • Kwamishinan shari’a na jihar, Barista Haruna Isah Dederi ne ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai
  • Barista Haruna Dederi ya yi martani ne kan hukuncin da Mai shari’a A.M Liman ya yanke game da dokar masarautun Kano ta 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta yi martani kan hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke a safiyar ranar Alhamis game da dokar masarautun jihar ta 2024.

Gwamnatin jihar ta ce hukuncin da Mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman ya yanke ya nuna cewa har yanzu Muhammadu Sanusi II ne Sarkin Kano.

Gwamnatin Kano ta yi magana kan hukunci kotu
Gwamnatin Kano ta dage kan cewa Muhammadu Sanusi II ne Sarkin Kano. Hoto: @Imranmuhdz Asali: Twitter

Kano: Gwamnati ta magantu kan hukuncin kotu

Kwamishinan shari’a na jihar, Barista Haruna Isah Dederi ne ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai a gidan gwamnati, in ji jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ta umarci ‘yan sandan jihar da su fitar da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga karamar fadar Gidan Nassarawa.

Jaridar Vanguard ta ruwaito Dederi ya ce ya kamata a fitar da Bayero daga karamar fadar domin gwamnati ta riga ta kammala shirye-shiryen rushewa da kuma gyara fadar.

"Har yanzu Sanusi II ne sarki" - Dederi

Sanarwar ta ce:

“A bisa hukuncin da kotun ta yanke, babu shakka ta sake tabbatar da ingancin dokar da majalisar dokokin jihar Kano ta zartar da sa hannun gwamnan jihar Kano a ranar 23 ga Mayu.
“Ƙarin ma’anar hukuncin shi ne, duk ayyukan da gwamnati ta yi kafin fitowar umarnin wucin gadi na kotun na nan daram. Haka kuma Muhammadu Sanusi II ne Sarkin Kano."

Ana zaman dari-dari a Kano

A wani labarin mun ruwaito cewa an fara zaman ɗari ɗari a Kano jim kadan bayan babbar kotun tarayya ta yanke hukunci kan dokar da ta rusa masarautun jihar.

A hannu daya kuma, an ga wani bidiyo da ya nuna yadda magoya bayan Aminu Bayero ke murna bayan kotun ta rusa nadin da aka yi wa Muhammadu Sanusi II.

Asali: Legit.ng

People are also reading