Home Back

Abin da ya kamata mutum ya yi a lokacin ambaliyar ruwa

bbc.com 2024/7/1

Asalin hoton, Reuters

.
Bayanan hoto, Tsaftace muhalli bayan ambaliya aiki ne da ke ɗaukar lokaci mai tsawo
  • Marubuci, Luis Barrucho
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Ambaliya ta rushe wurare da dama kuma ta raba dubban mutane da muhallin su a ƙasashe da yawa, daga farkon shekarar nan zuwa yanzu.

Bincike da yawa da aka yi sun nuna cewa sauyin yanayi yana ƙara haifar da ambaliyar ruwan daga lokaci zuwa lokaci, kuma ƙwararru sun yi gargaɗin cewa ana iya ci gaba da fama da wannan matsala.

Afghanistan da Brazil da Indonesia da Kenya da Oman da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa suna daga cikin ƙasashen da suka yi fama da mummunar ambaliyar ruwa a wannan shekarar.

A dukkan wuraren da aka samu ambaliyar, ruwa na tumbatsa har ya kori dubban mutane daga gidajen su.

A cikin wannan rahoton, mun yi duba kan dalilan da suka sa matsalar ambaliyar ta yawaita da kuma matakan kare kanku da sauran jama'a daga ambaliyar.

Mene ne ambaliyar ruwa?

Ambaliya tana daga cikin annobar da ke faruwa idan ruwan sama ya yi yawa har ya tumbatsa zuwa hanyoyin da ba nasa ba.

Ambaliya tana iya faruwa kowanne lokaci na shekara, amma sauyin yanayin da ake fama dashi yana ƙara kawo barazanar faruwar shi.

Wani nau'in ambaliya mai munin gaske itace wadda ke faruwa idan aka shiga yanayin zafi sosai, da kuma bushewar ƙasa.

Ƙungiya agaji ta British Red Cross ta yi bayanin cewa "Hakan na nufin idan aka shiga yanayi da ƙasa zata bushe sosai ta kuma kame kamar an ƙona ta. To idan aka yi ruwan sama mai ƙarfi, ƙasar ba zata iya shanye ruwan da sauri ba, domin haka sai ruwan ya kwanta a kan ƙasa. Wannan yanayi yana haifar da ambaliya sosai,"

Ambaliya tana janyo ɓarna mai yawa, kamar asarar rayuka da kuma kayayyaki, kodai na mutane ko kuma na gwamnati, irin su asibitoci da sauran su.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce daga 1998 zuwa 2017 ambaliya ta shafi mutune fiye da biliyan biyu a duniya baki ɗaya.

Majalisar Dinkin Duniya ta ƙara da cewa daga cikin wuraren da aka fi samun ambaliya akwai yankunan da gine-ginen su basu kan ƙa'ida, da kuma waɗanda suka tre hanyar ruwa.

Haka nan kuma, wuraren da babu tanadin hanyoyin fargar da mutane a kan ambaliya da kuma ƙarancin sani game da abubuwan da ke haifar da ambaliyar.

Asalin hoton, Reuters

.
Bayanan hoto, Masu aikin jin ƙai suna taimakawa a duk lokacin da aka samu ambaliya

Me ke janyo ambaliya?

Ana iya samun ambaliya saboda ruwan sama mai ƙarfi, ko narkewar ƙanƙara ko kuma mummmunar guguwa, musamman a gaɓar teku.

Ambaliyar da aka fi sani ta kasu gida uku:

  • Ambaliyar da ke faruwa saboda ruwan sama mai ƙarfin gaske, har ta cika rafi ko kogi ko kuma sauran magudanan ruwa ta yadda ruwa zai tumbatsa kuma fita daga hanyoyon sa.
  • Ambaliya daga rafi, inda rafin ke cika ya wuce ƙa'ida saboda ƙarfin ruwan sama, ko narkewar dusar ƙanƙanra.
  • Ambaliyar bakin kogi, wadda guguwar tsunami da iska mai ƙarfi ke haifarwa.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashi 80% zuwa 90% na annobar da ake samu a duniya, cikin shekara 10 da ta gabata tana da alaƙa da ammbaliya da kwararar hamada da guguwar tsunami da tsananin zafi da kuma iska mai ƙarfin gaske.

Asalin hoton, Reuters

.
Bayanan hoto, A watan Mayu, ambaliya ta kashe mutum 160, ta kuma raba wasu fiye da rabin miliyan da muhallin su a Brazil

Me ya sa ambaliya ke da haɗari?

Ambaliya tana tarwatsa gidaje, ta kawo cikas ga harkokin sufuri ta kuma durƙusar da kasuwanci.

Ƙungiyar agaji ta British Red Cross ta ce mutanen da ambaliya ta shafa suna tafka asarar muhallin su da kasuwancin su, kuma a lokuta da dama suna shafe kwanaki ko watanni ko ma shekaru suna neman tallafi.

Asalin hoton, Reuters

.
Bayanan hoto, Ɓarnar ambaliya

Haka nan kuma, ambaliyar tana iya gurɓata ruwa ya kuma yaɗa cutuka.

"Ambaliya tana iya jefa mutane cikin matsananciyar buƙatar abinci da muhalli da magunguna da tufafi da kuma kuɗi.''

Koda ga mutanen da ke da inshora, dole ne wannan matsala ta shafe su domin kuwa akwai dokokin da suka ƙayyade ko sau nawa mutum zai amfana da tsarin inshoran kayan da ya yi asara. Ga kuma tsada.

A misali, a Birtaniya, ana shafe shekara ɗaya ko fiye da haka kafin mutane su koma cikin gidan su bayan an samu ambaliya a gidan. Kamar yadda ƙungiyar masu inshora ta Birtaniya ta bayyana.

Wani rahoton BBC da aka wallafa a watan Mayu ya nuna cewa akwai kmfanoni da masana'antu fiye da 100 da ke jiran a biya su inshoran kayan da suka tafka asara fiye da watanni shida bayan wata mabaliya a arewacin Ireland.

A wasu sassan duniya da dama, waɗanda ambaliyar ta shafa basu da wani tanadi na samun inshorar.

Yadda ruwan sama mai ƙarfi ke janyo ambaliya

Yadda ambaliyar ruwa ke faruwa

Idan rafi zai yi ambaliya, yana ɗaukar lokaci yana nuna alama saboda a hankali yake cik har ya shanye gaɓar da aka tsara tare ruwan rafin.

Amma idan ruwan sama ne ya haddasa ambaliyar, tana faruwa ne cikin ƙanƙanin lokaci daga fara ruwan saman zuwa lokacin da wurare za su cika nhar a samu ambaliyar.

Hukumar hasashen yanayi ta Birtaniya ta ce "Ambaliyar ruwa ta fi faruwa a wuraren da rafi baya da faɗi sosai, yanayin da ke bai wa ruwa damar kwarara cikin sauri. Tana kuma faruwa a ƙananan ƙoramu da a gefen su akwai ko dai titin mota da aka yiwa kwalta, ko ginin kankare musamman a birane, inda yake da wahalar gaske a samu ƙasar wajen ta shanye ruwan da ya kwararo.''

Ta ƙara da cewa "A haka ne sai ruwan ya ci ƙarfin magudanan da aka yi, har ya yi ambaliya.''

Shuka bishiyoyi da ciyawa na taimakawa sosai wajen hana ambaliya, musamman a birane domin kuwa suna tsotse ruwan.

Yadda za ku kare kanku a lokacin ambaliya

Ƙwararru sun zayyana abubuwan da ya kamata a yi idan ambaliya ta faru:

  • Idan akwai barazana ga rayuwar wani ko wata, to a gagguta kiran lambobin agajin gaggawa domin samun ɗauki
  • Kada ku yi tafiya ko tuƙi cikin ruwan da yake ambaliya ko kuma neman shiga cikin ruwan domin tsallakewa. Ruwan yana zuwa da ƙarfin gaske ta yadda zai iya janye mota.
  • Kada a yi tafiya a kan katangar da ta kange rafi, ko kuma a gaɓar rafin
  • A guji duk wani abu da zai a shiga cikin ruwan da ke ambaliya domin kuwa zai iya yaɗa cutuka. Idan kuma har aka taɓa ruwn, to a gaggauta wanke hannu ko wajen da ruwan ya taɓa da ruwa mai tsafta
  • Kada a bari ƙananan yara su yi wasa a kusa da wajen da ake mbaliya

Asalin hoton, Reuters

.
Bayanan hoto, A watan Afirilu, ambaliya ta kusa shanye wata mota a Dubai

Me ya sa ake yawan samun ambaliya kuma take janyo hasara sosai?

Majalisar Dinkin Duniya ta ce "Ana hasashen ci gaba da samun ambaliya a duniya saboda matsalar sauyin yanayi da ake fama da ita".

Yawan ɗumamar yanayi da ake samu yana ƙara samar zafin rana da yiyuwar haɗuwar hadari da kuma saukar ruwan sama mai ƙarfi, a sassan duniya.

Hukumar kula da yanayi ta Birtniya ta ce "Idan ana cikin yanayi na zafi sosai, to iskar da ke kaɗawa tana ɗauke da ruwa a cikin ta, kuma hakan ke sawa idan aka yi ruwan sama a irin wannan yanayi sai a samu ruwan ya yi ƙarfi sosai saboda irin sinadaran da ke cikinsa.''

"Ana ci gaba da samun ɗumamar yanayi, ana ƙara samun ruwan sama mai ƙarfi, kuma yiyuwar samun ambaliya na ƙara bayyana.'' inji Hukumar kula da yanayi ta Birtniya.es.

Ilimin kimiyya na taimakawa wajen tantance abubuwan da ke haifar da ambaliya, kodai a duniya baki ɗaya ko kuma a wasu sassa.

Amma idan aka yi nazarin ambaliyar da aka yi a birnin Dubai na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, da kuma Oman a watan Afirilun 2024, da wuya a iya tantance ko sauyin yanayi ya na da kaso mai tsoka a abubuwan da suka janyo ambaliyar.

Wannan kuwa yana da alaƙa da yadda dama can a tarihi ba a cikin samun ruwan sama mai ƙarfi ba a wannan sashin na duniya.

Amma an tabbatar cewa ƙarfin ruwan saman da ake samu ya ƙaru da kashi 10 zuwa 40, kuma hakan na da laƙa da sauyin yanayi, kamar yadda hukumar kula da yanayi ta duniya ta bayyana.

Yadda zafi mai tsanani ke haifar da ruwan sama mai yawa

A cikin watan Afirilu an yi fama da ambaliy a Gabashin Afirka. Masana kimiyya suna bincike domin gano yadda sauyin yanayi ya bayar da gudunmuwa wajen samun wannan matsalar.

A watan Satumban 2023, an yi mummunar ambaliya a Arewacin Libya. Hukumar kula da yanayi ta duniya ta yi hasashen cewa sauyin yanayi ya sa ruwan saman da ake samu a ƙasar ya ƙaru da kashi 50 ko fiye da haka.

Ta kuma ce lamarin ya zo babu zato saboda matsalar tsaro da ta ɗaukewa hukumomi hankali.

Hukumar kula da yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana samun ƙaruwar ruwn sama mai ƙarfin gaske a sassan duniya saboda ayyukan da mutane ke yi masu janyo ɗumamar yanyi.

Ta kuma yi gargaɗin ci gaba da samun wannan matsala har zuwa lokacin da aka samu canji.

People are also reading