Home Back

WUTA A KUDU MASO GABAS: ‘Yan bindiga sun bindige Sojojin Najeriya 4 a garin Aba, sun banka wa motar su wuta

premiumtimesng.com 2024/6/29
WUTA A KUDU MASO GABAS: ‘Yan bindiga sun bindige Sojojin Najeriya 4 a garin Aba, sun banka wa motar su wuta

Aƙalla Sojojin Najeriya huɗu aka kashe ranar Alhamis a garin Aba, babban birnin Jihar Abiya.

Aba ne gari mafi ƙarfin hada-hadar kasuwanci a yankin Kudu maso a Najeriya.

PREMIUM TIMES ta ji cewa ‘yan iskan gari kamar su 15 ne suka kai wa sojojin farmaki wajen ƙarfe 8 na safiyar yau Alhamis, a wani shingen binciken kan titi a Mahaɗar Titina dake Obikabia, cikin garin Aba.

An ce ‘yan bindigar su na tirsasa wa kowa ya zauna a gida tilas, kamar yadda ƙungiyar taratsin a-ware ta IPOB ta bada umarni a yankin na jihohin Kudu maso Gabas, domin tunawa da zagayowar ranar Biafra, wadda a kowace shekara ake murnar zagayowar ta a yankin.

Wanda aka yi kisan kan idon sa mai suna Marvelous ya shaida wa wakilin mu cewa maharan waɗanda suka rufe fuskokin su, sun dira wurin kuma nan take suka buɗe wa sojojin wuta.

Marvelous ya ce an kashe sojoji huɗu, wani soja ɗaya kuma ya ji mummunan rauni.

“An kashe soja huɗu. Ɗaya kuma an ji masa rauni da harbin bindigar da aka yi masa.” Inji Marvelous, Wanda yayi magana da wakilin mu da Turancin ‘pidgin’.

Maharan su na cikin baƙar Highlander (SUV). Har wasu farar hula su ma an ji masu raunuka yayin harbin.” Inji shi.

Dama an riƙa nuna wani bidiyo a soshiyal midiya, wanda ke ɗauke da waɗanda suka kai wa sojojin hari a cikin baƙar mota.

PREMIUM TIMES ta kalli bidiyon, kuma ta lissafa aƙalla mahara 10.

Har yanzu dai sojoji ba su ce komai ba tukunna.

People are also reading