Home Back

Eid-el-Kabir: Sarkin Musulmi Ya Nemi Al’umma Su Nemi Watan Zul-hijja Daga Gobe Alhamis

leadership.ng 2024/7/5
Eid-el-Kabir: Sarkin Musulmi Ya Nemi Al’umma Su Nemi Watan Zul-hijja Daga Gobe Alhamis 

Gabanin bikin Eid-el-Kabir na bana, Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA) kuma Sarkin Musulmi, Mai Alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bukaci al’ummar Musulmin Nijeriya da su sanya ido kan ganin jinjirin watan Zul-Hijja 1445AH bayan faduwar rana a ranar Alhamis 29 ga watan Zul-Qa’dah 1445AH, daidai da ranar Alhamis 6 ga watan Yuni 2024.

Sultan Abubakar III ya bada umarnin ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakin babban sakataren hukumar ta NSCIA, Farfesa Salisu Shehu a ranar Laraba.

Ya bayyana cewa: “A kimiyance, lokacin da ake sa ran fitowar wata shi ne ranar Alhamis, 6 ga Yuni, 2024 da karfe 1:38 na rana a agogon Nijeriya.

Watan Zul-Hijja, wata na 12 kuma na karshe a cikin kalandar Musulunci, yana daya daga cikin watanni hudu masu alfarma a Musulunci da musulmin duniya ke gudanar da aikin hajji da bukukuwan Sallah Eid-El-Kabir.

A cikin wannan wata ne alhazan musulmi daga sassa daban-daban na duniya ke taruwa a birnin Makkah na kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin da za a fara a ranar takwas ga wata, da kuma gudanar da bukukuwan Sallah daga ranar 10 zuwa 13 ga watan Zul Hijjah.

People are also reading