Home Back

Rikicin Sarauta: Dalilin da Ya Sa Har Yanzu Aminu Ado Bayero Ne Halastaccen Sarkin Kano

legit.ng 2024/7/6
  • Wani lauya a jihar Kano, Umar Sa'ad Hassan, ya yi bayanin cewa har yanzun Alhaji Aminu Ado Bayero ne halastaccen Sarkin Kano
  • Hassan ya bayyana cewa babbar kotun tarayya mai zama a jihar ta ba da umarnin dakatar da mayar da Muhammadu Sanusi kan sarauta
  • A wata hira da Legit Hausa, Hassan ya ce Aminu ne sarkin Kano har sai lokacin da gwamnatin jihar ta ɗaukaka ƙara kuma aka jingine umarnin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Wani kwararren mai shiga tsakani kuma masanin doka, Umar Sa'ad Hassan ya ce har yanzu Aminu Ado Bayero ne Sarkin Kano a doka.

Hassan ya bayyana cewa sarki na 15, Alhaji Amunu Ado Bayero ne halastaccen sarkin Kano ba Muhammadu Sanusi II ba.

Muhammadu Sanusi, Abba Kabir da Aminu Ado Bayero.
Lauya ya yi bayanin cewa har yanzu Aminu Ado ne sarkin Kano Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Abba Kabir Yusuf Asali: Facebook

Ya yi bayanin cewa babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta bayar da umarnin a dakatar da sabuwar dokar masarauta wadda majalisar dokokin jihar ta yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan ya ƙara da cewa kotun ta kuma dakatar da mayar da Muhammadu Sanusi II a kan karagar Sarkin Kano.

A cewar Hassan, Sarki Aminu Ado na nan a matsayin basaraken birnin Kano har sao lokacin da gwamnatin jihar ta ɗaukaka ƙara kuma kotu ta soke umarnin.

Hassan ya ce ƙarar da gwamnatin Kano ta kai kotu da ke da iko iri ɗaya da babbar kotun tarayya cin mutuncin shari'a ce.

"Babban Kotun Tarayya ta dakatar da amfani da sabuwar dokar masarautar da kuma sake mayar da Sanusi II.
"Duk wanda ke da korafi wane iri ne ya je kotun ko kuma ya daukaka kara ba wai ya nemo wani umarnin daga kotu mai daraja daidai da wannan ba.
"Hakan rashin mutunta kotu ne kuma matakin da alkalin alƙalan Najeriya ya ɗauka shi ne daidai. Maganar gaskiya Aminu Ado ne Sarkin Kano yanzu haka."

A karshe ya ce tun da tsagin Aminu Bayero ne suka shigar da ƙarar, dole ne sai kotu ta tabbatar kuma ta amince da mayar da Sanusi kafin ya iya zama sarkin Kano.

Asali: Legit.ng

People are also reading