Home Back

'An samu ƙaruwar satar mutane a Najeriya'

bbc.com 2024/7/5
.

Asalin hoton, Getty Images

A Najeriya, wani rahoton da kamfanin Beacon Consulting da ke nazarin tsaro a Afirka ta yamma da yankin Sahel ya fitar ya nuna cewa a watan Mayun da ya gabata an samu ƙaruwar satar mutane domin kuɗin fansa a Najeriya idan aka kwatanta da Afrilun wannan shekara.

Rahoton ya ce adadin na satar da jama'a ya nunka har kusan sai uku, tsakanin Afrilu zuwa Mayun bana kuma matsalar satar jama'a domin neman kudin fansa ta fi ƙamari a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Rahoton ya ce amfani da ƙarfi kawai ba zai iya magance matsalar tsaron Najeriya ba muddin ba a magance talauci da ya yi wa mutane katutu ba.

Shugaban kamfanin Dr Kabir Adamu, ya shaida wa BBC cewa a watan Mayu kaɗai da ya gabata mutum kusan 1, 090 ne suka mutu, rangwamen mutum 7 idan aka kwatanta da Afrilu.

Ya ƙara da cewa “Da muka duba batun satar mutane daga kan 311 da aka samu a watan Afrilu ya ƙaru a watan Mayu zuwa 1, 128, wanda ya nunka da kashi 268 cikin ɗari.

"Da muka raba yakunan mun lura cewar arewa maso gabas ne ke kan gaba sannan sai arewa maso yamma da ke biye mata, wanda idan ka haɗa shi da sauran yankin arewacin kasar zaka ga shi ne yanki da ke kan gaba wajen fama da matsalar garkuwa da mutane” inji Dr Kabir.

Ya kuma ƙara da cewar a jihohi kuwa Jihar Borno ce ke ka gaba, sai Zamfara, da Kaduna sai kuma Katsina da sauran jihohin da ke arewacin kasar“

Sannan ya ce wani abu da ya ba su mamaki shi ne yadda aka samu karuwar satar mutane don neman kudin fansa a babban birnin ƙasar Abuja.

Ya ce a watan Afrilun da ya gabata bayanan da suka samun na satar mutum uku zuwa huɗu ne, yayin da a watan Mayu kuma ya karu zuwa mutum 50 a yankuna 6 da ake da su na babban birinin.

Ta wacce hanya za a shawo kan matsalar?

Dakta Kabiru Adamu, ya ce matakan da gwamnatin ƙasar ke ɗauka ba sa tasiri sosai wajen shawo kan matsalar da ta zamewa kasar karfen kafa, don haka dole ne a sake bijiro da wasu sabbin hanyoyi.

Sannan ya shawarci gawamnati da ta sauya salon yadda ta ke ɗauka na amfani da ƙarfi, inda ya ce hakan ba ya tasiri, maimakon hakan magance matsalolin da ke haifar da satar mutanen shine abun da ya fi.

“Akwai bukatar daukar matakai kan ɗumamar yanayi, saboda irin abin da ɗumamar yanayi ke haifarwar, da talauci da ya yi katutu a kasa, da makamai da ke yawo a tsakanin al’umma, da yadda kan iyakokin mu suke a bude, inda ana iya shigo da komai, da matsalar miyagun kwayoyi da suka yawaita'' inji shi.

Haka kuma ya ce akwai buƙatar gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi kokarin hada kai tsakanin ta da gwamantocin jihohin kasar wajen magance matsalar tsaron, tare kuma da saka al’umma wajen tattarar bayanai da tantance shi.

People are also reading