Home Back

Girman Darajar Manzon Allah (SAW) Da Allah Ya Yi Rantsuwa Da Ita (6)

leadership.ng 2024/5/17
Manzon Allah

Malam ibn Ada’ir ya ce cikin fadar Allah (SWT) cewa Allah ya yi rantsuwa da Alfijir da darare goma. Yadda zahirin ayar yake tana nufin ranar Sallah babba, da kuma kwanaki goma na watan Zulhijja, amma wannan Alfijir din yana nufin Annabi Muhammadu (SAW) domin daga shi ne Imani ya bubbugo.

Idan muka dubi Fasali na biyar (na Littafin Ashafa) cikin rantsuwar da Allah (SWT) wanda girmansa ya daukaka ya yi don tabbatar da matsayinsa (Manzon Allah SAW) a wajensa, Allah (SWT) ya saukar da sura guda don daukaka sunan Manzon Allah (SAW). “Suratut Duha”, “Alam nasharah”, “Suratul Kausar”, wadannan surorin na Manzon Allah (SAW) ne da Allah ke fadan irin abubuwan da ya yi masa. Kodayake dukkan surorin Alkur’ani duk nasa ne (Manzon Allah) amma dai ba kamar wadannan surorin musamman “Surat Duha” saboda sanda ta sauka sai da Manzon Allah (SAW) ya yi kabbara kuma duk Makka sai da aka ji wannan kabbaran da Manzon Allah (SAW) ya yi, shi ya sa ko karatun Kurani ake yi idan an fado ta sai an yi kabbara don tuna wannan ranar. Allah ya yi ranstuwa da rana lokacin walaha, shi ne hantsi da ake cewa, kamar karfe 8 zuwa 11 na safe, ko daga karfe 10 zuwa 11 kafin rana dai ta zo tsakiyar sama.
To Allah ya yi rantsuwa da Duha da kuma dare idan ya lullube. Wannan yana daga cikin hikimar Alkur’ani ne, saboda Manzon Allah (SAW) bai taba zama cikin bata ba shi ya sa Allah ya fara masa da rana kafin dare, Amma Sayyidina Abubakar shi kuma an fara masa da dare kafin rana saboda zama cikin duhu da ya yi kafin zuwan Musulunci.

Malamai sun ce akwai hikima cikin yin hakan saboda lokacin da aka haifi Dan Adam sai da Allah ya sa aka yi ta masa ruwan bakin ciki har tsawon shekara 300, kafin nan Allah ya sa aka yi masa ruwan farin ciki, saboda haka Dan Adam ko ya yi farin cikin tsawon wasu lokuta sai bakin ciki ya biyo baya don shi ya fi yawa, saboda haka ake so ya rinka yawan addu’a.

Malaman Tafsiri sun yi sabani cikin sababin saukar ita wannan surar saboda Hadisai da suka zozzo da aka ce Manzo (SAW) ya yi kwana biyu bai fita Sallar dare ba, dama Ka’aba yake fitowa cikin dare ya yi ta karatu a farkon Musulunci, ayoyin da duk suka saukan masa to su zai yi ta karantawa su kuma kafiran Makka abin ba ya musa dadi, sai kuma kwana biyu shiru bai yi ba, saboda wahayi bai sauka masa ba, to sai wata mace ta yi magana (ita ce Ummu Jamilu matar Abu Lahabin) ta zo ta ce “Muhammadu shin aljanin nan da yake kawo maka maganganun ko ya kyale ka ne? Shi ma kanshi ya gaji; kai har mun huta”. To kila wannan ce ta jawo sababin saukar wannan ayar, kila kuma su mutanen Makkan bakidaya suka ce “kai shi yanzu Muhammadu Ubangijin nasa ma ya gaji da shi kullum ya hana mu sakat ya hana mu komai, ga shi Ubangijin nasa ma ya yi fushi da shi ya daina saukar masa da komai”.

Da Annabin kirkirar abun yake da kansa; da ya kirkiro wani abun ya fada saboda haushin tsayawar saukar wahayin. Abdullahi ibn Abbas ya ce kwana 15 aka yi, Katadatu ya ce gurin kwana 40 aka yi, kila kuma kafuran su suka ringa tsokanansa suna cewa “toh ya Muhammad ya ya muka ji ka yi shiru ne kwana biyu, shin wani abun bai sauka ba?”, wasu kuma su ce Shaidanin sama ya bar shi. Wasu kuma su ce Ubangijin sama ya barshi saboda su waka suka sani (don mai wakar sharri shaidan ne zai rika fado masa fasahar sharri, shi kuma mai wakar alkhairi Sai Allah ya hada shi da Jibrilu ya ringa fado masa fasahar alkhairi), to su sharri kawai suka sani. Saboda Manzon Allah (SAW) ya damu sosai sai Allah ya saukar masa da “Suratut Duha”.

A cewar Malami masanin addini, Alkadi Iyad (Allah ya yarda da shi), wannan aya ta kumshi girmamawan Allah ga Annabi (SAW) da daukaka darajarsa. Ayar ta tattara daraja da girma guda shida wanda Allah ya yi ma Annabi (SAW) a cikinta. Na farkon shi ne Allah ya yi mai rantsuwa “Wadduhe”, har ma Allah ya nuna masa cewa ya yi rantsuwa da Ubangijin Rana da Dare cewa “Wallahi ban barka ba”. Yana daga girman daraja da kyauta da Allah ya yi masa (SAW), sai da Allah ya rantse ya ce masa “kafuran nan abin da suka fada karya suke, ni ban barka ba”. Daraja ta biyu ita ce bayanin girman Manzon Allah (SAW) da darajarsa da ranbantarsa wajen Allah, bisa fadin Allah Ubangiji cewa “bai barka ba kuma ban ki ka ba”, kila fassarar tana nufin ma’anar Ubangijinka bai barka banza ba, tun kana yaronka kana maraya bai barka banza ba, bai bar kula da lamuranka ba bayan ya zabe ka. Daraja ta uku: fadin Allah ga Manzon sa (SAW) a cikin surar, Ibn Is’haka ya ce ana nufin “Ai makomar ka a Lahira ita ce mafi girma”, saboda duk wanna girman da ya bashi a duniya to a can lahira ya fi saboda can zai yi ceto ma.

Ibn Is’haka ya ce ai makomar wajen Allah ya fi abin da Allah ya ba ka daga girman duniya. Shi kuwa Sahalu ya ce ai Allah yana nufin “na ajiye maka daga ceto, sannan matsayin da za ka tsaya daga ceto shi yafi maka da duk matsayin da za ka tsaya a Duniya.

Abu na hudu: fadin Allah (SWT) “da sannu Ubangijinka zai ba ka har ka yarda”. Wannan aya mai tattarewa ce cikin dukkan fuskokin girmamawa, Manzon (SAW) Allah Bawan Allah ne amma ga shi yau Allah yana cewa zan baka har sai ka yarda, wato kamar Ubangiji yana neman yaddar sa (SAW), to wannan girmamawa ta kai girmamawa! Nau’o’in arziki da mabambatan ni’imomin Duniya da Lahira da dadi. Dan Is’haka ya ce ai Ubangijinka zai yardar da kai da rambanta a nan duniya duk abin da kake so ya faru addininka ya game ko ina, al’ummarka su hau kan kowace al’umma duk abin da ka nema Allah zai ba ka sai dai abin da Allah da kansa ya gaya maka, wannan banda shi.

Akwai ranar da Manzon Allah (SAW) ya yi sujjada har sai da Sahabbai suka ji tsoro sannan ya taso ya ce “Sujjadar godiya nake yi, Allah ya ce na yi addu’a na yi guda uku, ya karbi guda biyu amma dayan kaddararshi ta rigaya”. To shi ya sa aka sa wa wajen ma Masjidil I’ijawa saboda akwai hikima a cikin yin hakan, da lada kuma a Lahira. Kila kuma zai bashi tekun nan na Alkausara da kuma ceto.

An karba daga ba’arin (sashen) ‘ya’yan gidan Annabi (SAW) (Imamu Sa’alabi a tafsirinsa ya ce daga Sayyidi Ali), Sayyidina Ali ya ce ba wata aya a cikin Kur’ani da take sa mutum ya kaunaci Rahamar Allah ta debe wa mutum kewa irin wanna ayar, saboda Dan Wahashi ya aiko wa Manzon (SAW) yana son zai musulunta amma yana tsoron kashe Sayyidina Hamza (RA) da ya yi da kuma zunubansa a jahiliyya, sai Manzo (SAW) ya aika masa da wannan ayar, duk da shi aka aika wa amma ta zama ba ta Wahashi ce kadai ba ta dukkan al’umma ce. Allah ya ce Ya Muhammad (SAW), ka gaya musu (in ji Allah) “ya bayina wadanda suka yi laifi kar ku debe tsammani da rahamar Allah, Allah yana gafarta zunubi duka”. Ka ga kar mutum ya yi tunanin zunubi zai hana shi shiga Musulunci ko kuma shi Musulmi ya yi zaton zunubi zai hana shi samun Rahamar Allah. A’a, Allah yana son a ringa mai kyakkyawar zato.

Toh haka Sayyidina Ali ya ce ita ayar “Wala saufa yuu dika Rabbaku Fatardaa” har ta fi waccan ayar ma. Ya ce babu aya cikin Alkur’ani da za ta sa a kaunaci Rahamar Allah irinta. Ka san kuwa Manzo (SAW) ba zai yarda wani daga cikin alkummarsa ya shiga wuta ba; haka kuma Manzon Allah (SAW) shi zai yi ceto ranar Lahira, wadansu ma har sai sun shiga wuta, Manzo (SAW) zai ceto su, marar “La ilaha illahi” wato Kairi shi kadai ne zai dawwama a wuta, wa iyazu billahi. Allah ya sa muna daga cikin wadanda Manzon Allah (SAW) zai ceta tun a sahun farko.

A mako mai zuwa za mu cigaba daga inda muka tsaya cikin yardar Allah (SWT). Wa sallallahu alal fatihil khatimil hadi wa ala alihi hakka kadrihi wa mikdarihil aziym.

People are also reading