Home Back

Tsohon Hadimin Shugaban Ƙasa Ya Kawo Mafita Kan Mafi Ƙarancin Albashi a Jihohi

legit.ng 2024/7/6
  • Doyin Okupe, tsohon daraktan kamfen Peter Obi ya bukaci a cire gwamnoni daga dokar mafi ƙarancin albashi ta tarayya
  • Okupe, tsohon hadimin shugaban kasa ya ce kamata ya yi a bar kowace jiha ta yanke abin da za ta iya biyan ma'aikata
  • A cewarsa, ba zai yiwu abin da jihar Legas ta biya a matsayin mafi karancin albashi, shi jihar Sakkwato za ta biya ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon hadimin shugaban kasa, Doyin Okupe, ya caccaki dokar mafi karancin albashi ta kasa.

Okupe ya soki dokar yadda ta wajabta wa gwamnonin jihohin Najeriya 36 su rika biyan ma’aikata mafi karancin albashi a jihohinsu daidai da na gwamnatin tarayya.

Doyin Okupe.
Tsohon hadimin shugaban ƙasa ya nemi a cire gwamnoni a dokar mafi ƙarancin albashi ta kasa Hoto: Doyin Okupe Asali: Facebook

Tsohon daraktan yakin neman zaɓen Peter Obi ya yi wannan furucin ne a cikin shirin siyasa a yau na Channels tv ranar Jumu'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa kamata ya yi a bar kowane gwamna ya yanke adadin kuɗin da zai iya biyan ma'aikata a matsayin mafi ƙarancin albashi.

A ruwayar Daily Post, Okupe ya ce:

"Bai kamata mu yi wannan doka ba wadda ta wajabtawa gwamnoni yin biyayya ga adadi ɗaya.
“Abin da nake nufi alal misali idan kuna biyan mafi karancin albashi a Legas, me zai sa na biya irin haka a Sakkwato? Ina ganin a bari kowane gwamna ya yanke abin da zai iya a jiharsa."

Ya ce abin da ya kamata Shugaban kasa ya nayar da hankali shi ne hwamnatin tarayya, su kuma jihohi su zauna da ƴan kwadago na jihohi su yanke abin da ya dace.

An shafe watanni da dama ana takun saka tsakanin ma’aikata da gwamnatin tarayya kan sabon mafi karancin albashi.

Bayan wa'adin da ƴan kwadagon suka sanya ya ƙare ranar 31ga watan Mayu, NLC ta ayyana shiga yajin aiki ranar Litinin 3 ga watan Yuni, ta rufe harkokin kasuwanci a faɗin ƙasar nan.

Sai dai an dakatar yajin aikin a ranar Talata bayan da gwamnatin tarayya ta yi alkawarin kara mafi karancin albashi zuwa fiye da Naira 60,000.

Bayan haka ne gwamnonin jihohi 36 suka fito suka bayyana cewa ba za su iya biyan N60,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ba.

Zulum ya mayar da ƴan gudun hijira gidajensu

A wani labarin Gwamna Babagana Umaru Zulum ya fara kashin farko na shirin mayar da ƴan gudun hijira gidajensu a kananan hukumomi 9 na Borno.

Ya kuma raba masu maƙudan kudi da suka kai N954.7m sannan kuma ya ba su kayayyakin abinci domin su sake gina rayuwarsu.

Asali: Legit.ng

People are also reading