Home Back

Liverpool Ta Amince Da Daukar Arne A Matsayin Sabon Kocinta A Kaka Mai Zuwa

leadership.ng 2024/5/18
Liverpool Ta Amince Da Daukar Arne A Matsayin Sabon Kocinta A Kaka Mai Zuwa

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta kulla yarjejeniyar daukar kocin Feyernood, Arne Slot a matsayin sabon kocinta wanda zai jagoranci kungiyar a kakar wasa mai zuwa bayan da Jurgen Klopp, ya bayyana aniyarsa na ajiye aiki a karshen kakar wasa ta bana.

Yanzu haka Arne shi ne mai horar da kungiyar Feyernood, inda Liverpool ta amince ta biya kudi har Yuro miliyan 9.4 domin dauko shi daga kungiyar ta kasar Holland.

Liverpool tana matsayi na uku a kan teburin gasar Firimiyar Ingila wanda Arsenal ke jagoranta, Atalanta ce ta kori Liverpool daga gasar UEFA Europa da ci 3-1 a wasan gida da waje.

People are also reading