Home Back

An sami Hunter Biden da mallakar bindiga ba bisa ka'ida ba

dw.com 2024/7/6
Hunter Biden dan shugaban Amurka Joe Biden
Hunter Biden dan shugaban Amurka Joe Biden

Nan gaba ne dai ake sa ran mai shari'a Maryellen Noreika zai baiyana hukunci kan karar.

Mutane goma sha biyu masu taimaka wa alkali yanke hukunci sun tafka muhawara kan karar yayin da su ma lauyoyi masu kare wanda ake tuhuma suka kammala bayar da nasu bahasin a shari'ar da aka gudanar a birnin Wilmington da ke jihar Delaware.

Ana tuhumar Hunter Biden ne da bayar da bayan karya a lokacin da ya sayi bindiga a watan Oktoban 2018 inda ya boye gaskiyar cewa shan kwaya ya zame masa jiki a lokacin. Zai iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 25 a gidan yari.

Shugaba Joe Biden ya ce ya amince da sakamakon shari'ar kuma zai ci gaba da martaba hukuncin shari'a a yayin da dansa wanda bai amsa laifinsa ba ya ke nazarin daukaka kara.

People are also reading