Home Back

Ƴan Bindiga Sun Harbe Shugaba A Jami’ar UDUS

leadership.ng 6 days ago
Ƴan Bindiga Sun Harbe Shugaba A Jami’ar UDUS

Wasu ‘yan bindiga sun kashe Farfesa Yusuf Saidu, mataimakin shugaban jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto (UDUS), mataimakin shugaban sashen bincike, kirkire-kirkire da ci gaba. Lamarin ya faru ne a lokacin da yake tafiya daga jihar Sokoto zuwa jihar Kaduna.

Jami’ar ta sanar da rasuwarsa ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Litinin, inda ta bayyana nagarta, da sadaukar da kai, da jajircewarsa.

Al’ummar jami’ar na ci gaba da jimamin rashin Farfesa Sa’idu, inda suka bayyana hakan a matsayin wani gagarumin rashi ga cibiyar da kuma duniyar ilimi.

Sanarwar ta jajantawa iyalansa da abokan aikinsa, tare da yi masa addu’ar Allah ya jikansa da rahama, ya gafarta masa zunubansa.

People are also reading