Home Back

Ginin Makaranta Ya Rufta A Jos, Ɗalibai Da Dama Sun Maƙale

leadership.ng 2024/8/24
Ginin Makaranta Ya Rufta A Jos, Ɗalibai Da Dama Sun Maƙale

Wani ginin makaranta a yankin Busa Buji, ƙaramar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato, ya rufta, inda ya bar ɗalibai da dama a maƙale. Wannan mummunan al’amari ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na safe a yau Juma’a, yayin da ɗalibai ke tsaka da rubuta jarabawa.

Ginin makarantar Saint Academy ya yi ruftawar da ta jawo tsoro da firgici tsakanin iyayen ɗaliban, waɗanda suka yi ta tsere zuwa wurin da abin ya faru cikin ruɗani don ganin ko ya rutsa da ƴaƴansu.

A halin yanzu ana gudanar da aikin ceto tare da taimakon jami’an tsaro, ciki har da Sojojin da ƴan sanda. Motar ceto da aka kawo domin taimakawa cikin aikin ta maƙale a cikin ƙasa, wanda ya ƙara tsananta al’amuran. Akwai rahotannin da ba a tabbatar ba na mutuwar wasu daga cikin waɗanda suka makale, duk da cewa an kai wasu ɗalibai da suka ji raunin asibiti domin samun kulawa.

Sashen da ya rufta ya haɗa da azuzuwan ɗaliban SS1, SS2, da SS3. Hankalin jami’an ceto ya karkata wajen ceto waɗanda har yanzu suke maƙale da kuma ba da kulawar lafiya ga waɗanda suka ji rauni yayin wannan rahoto.

People are also reading