Home Back

Zamu baza jami’an mu a lungu da saƙo dan kawar da masu ƙwacen Waya a lokacin Sallah – Rundunar tsaro ta KOSSAP

dalafmkano.com 2024/7/4

Rundunar tsaro mai yaƙi da ɓata gari masu ƙwacen waya, da magance matsalar faɗan Daba, da shaye-shaye, ta Aunty Phone Snaching da ke nan Kano, ta ce jami’an ta za su shiga lungu da saƙo na cikin birnin Kano, a wani ɓangare na magance matsalar tsaro yayin bikin babbar Sallah.

Kwamandan rundunar ta KOSSAP, a nan Kano, Inuwa Salisu Sharaɗa, shine ya bayyana hakan yayin zantawar sa da manema labarai, ya kuma ce kasancewar an hana hawan Sallah a jihar nan, ɓata gari za su iya amfanin da hakan domin su shiga cikin unguwanni domin ƙwacen wayoyin mutane da kuma aikata laifuka, a dan haka ne suka baza jami’an su domin samar da tsaro.

“Matasa ku rungumi zaman lafiya a yayin, da lokacin, da kuma bayan bikin babbar Sallah, domin duk wanda muka kama da aikata wani laifi da zarar mun kammala bincike zamu gurfanar da shi a gaban Kotun tafi da gidan ka da gwamnatin Kano, ta tanadar mana, “in ji Inuwa”.

Inuwa Salisu Sharaɗa, ya kuma shawarci iyaye da su ƙara kulawa da shige da ficen ƴaƴan su, domin gujewa faɗawar su cikin halin da bai kamata ba.

People are also reading