Home Back

RIKICIN SARAUTAR KANO: An ji ƙarar rugugin harbe-harben bindiga daga fadar Sarkin Kano a cikin dare zuwa asuban Talata

premiumtimesng.com 2024/7/2
RIKICIN SARAUTAR KANO: An ji ƙarar rugugin harbe-harben bindiga daga fadar Sarkin Kano a cikin dare zuwa asuban Talata

A daren ranar Litinin ne aka ji karar harbe-harbe a karamar fadar da tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ke zaune a Nasarawa GRA na babban birnin jihar.

Fadar tana da nisan kimanin mita 300 daga gidan gwamnatin Kano inda aka takaita zirga-zirgar ababen hawa zuwa wani bangare na hanyar da zai kai ka Tarauni.

A ranar Lahadin da ta gabata ne wasu mafarauta dauke da muggan makamai a fadar Sarkin da aka dawo da Sarki Lamido Sanusi, suka yi yunkurin kai farmaki kan wasu masu zanga-zangar neman gwamnan ya bi umurnin kotu da ya hana ta tsige Ado-Bayero.

Wasu mazauna yankin da masu wucewa sun yi zargin cewa an yi harbin ne don hana duk wani yunkurin kama Ado-Bayero bayan wata babbar kotun jihar ta bayar da umarnin a kore shi daga fadar a ranar Litinin.

Har yanzu ba a iya tabbatarwa ko harbe harben daga jami’an tsaro ne ko kuma dogaran fadan sarki.

Umarnin kotu da a kori Ado-Bayero daga fadar sarkin Kano

Babbar kotun jihar Kano ta umarci ‘yan sanda da su kori tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero daga fadarsa Nasarawa da yake zaune.

Kotun ta kuma umarci Ado-Bayero da takwarorinsa hudu a Masarautun Bichi, Rano, Gaya da Karaye da su daina bayyana kansu a matsayin sarakuna.

Kotun ta bayar da umarnin ne a ranar Litinin bisa karar da babban mai shari’a na jihar Kano, Kakakin majalisar dokokin jihar Kano, da majalisar suka gabatar a gabatanta.

Idan ba a manta ba, wata babbar kotu a Kano ta dakatar da gwamnatin Abba-Yusuf daga rushe masarautun jihar Kano da kuma naɗa Muhammed Sanusi II sabon sarki.

Sai dai kuma a zaman kotu a Kano eanar Litinin, ta bada umarnin ƴan sanda su kori, Aminu Ado daga gudan sarautan Kano sannan su tabbata baya nuna kansa a matsayin sarki a Kano har sai bayan kotu ta saurari karar da aka shigar a gabanta.

People are also reading