Home Back

Shugaba Biden ya soki Kotun Ƙolin Amurka kan bai wa Donald Trump kariya

bbc.com 3 days ago
Joe Biden

Asalin hoton, Getty Images

Shugaba Biden na Amurka ya Alla-wadarai da hukuncin da Kotun Kolin kasar ta yi na cewa tsofaffin shugabannin kasar ciki har da Donald Trump, suna da kariya 'yar takaitacciya daga gurfanar da su gaban kotu a kan aikata wani mugun laifi.

Shugaban ya ce hukuncin ya sa shi fargaba da tsoro, inda yake jiye wa dumukuradiyyar Amurka.

Da yake mayar da martani game da hukuncin kotun kolin a fadarsa ta White House, Shugaban na Amurka, ya ce hukuncin karen-tsaye ne ga tsarin nan na doka ta yi aiki a kan kowa.

Mista Biden ya ce a yanzu wannan hukunci zai karfafa wa Donald Trump gwiwa ya yi duk abin da yake so gaba-gadi.

Kazalika ya ce, hukunci ne mai hadarin gaske ga kasar, da zai share fagen saka da mugun zare a nan gaba, a ce shugaba zai kasance yana da kariya daga gurfana a gaban kotu kan tuhumar aikata mugun laifi, ya ce hakan cin fuska ne ga Amurkawa.

Ya ce : ''An kafa wannan kasa ne a kan tsarin – babu wasu saraki a Amurka. Dukkaninmu daya muke a gaban sharia.

Ba wani, ba wani mutum da ya fi karfin doka. Kai ba ma shugaban Amurka ba.

Hukuncin kotun kolin na yau na kariya ga shugaban kasa, ya canza wannan. Hukuncin na yau kusan kawai yana nufin babu iyaka kan abin da shugaban kasa zai iya yi.’’

Shi kuwa tun da farko tsohon shugaban kasar Donald Trump ya bayyana hukuncin ne na ranar Litinin a matsayin babbar nasara ga dumukuradiyya,

Rinjayen alkalan kotun kolin ta Amurka ya zartar da cewa shugaba yana da rigar kariya a kan abubuwan da ya yi na hukuma, amma kuma ba shi da kariya a kanb wadanda ya yi ba na hukuma ba, sannan suka mayar da batun ga alkalin da zai yi shari'a a kai.

Wannan hukunci a yanzu zai kara haifar da jinkiri a kan shariar Donald Trump ta zargin da ake yi masa na kokarin sauya sakamkon zaben shugaban kasar na 2020, wanda ya bai wa Biden nasara.

Da wannan hukuncin yanzu ya rage ga alkalin da zai yi shariar ya duba ya ga wadanne abubuwa ne Mista Trump ya yi a matsayinsa na shugaban kasa, wanda wannan abu ne da zai dauki watanni.

Hakan kenan zai iya sa da wuya a fara masa shari'a kafin zaben shugaban kasar da za a yi a watan Nuwamba, zaben da Trump din zai yi wa jamiyyarsa ta Republican takarar neman sake komawa kan shugabancin Amurkar.

People are also reading