Home Back

Kenya Ta Dakatar Da Yi Wa Ma’aikatan Gwamnati Karin Albashi

leadership.ng 2 days ago
Kenya Ta Dakatar Da Yi Wa Ma’aikatan Gwamnati Karin Albashi

Hukumar Albashi da Jin Dadin Ma’aikata ta Kenya, ta janye shirinta na kara albashin ‘yan siyasa masu rike da madafun iko daga 1 ga watan Yuli.

Kenya ta dakatar da shirinta na kara albashin ‘yan siyasa masu rike da madafun iko daga 1 ga watan Yuli.

A ranar Laraba ne Hukumar Kula da Albashi da Jindadin Ma’aikata ta bayyana cewa ta “dakatar da shirin kara albashin dukkanin ‘yan siyasa masu rike da madafun iko, kuma za ta yi duba ga shawara kan albashin dukkanin ‘yan siyasa don tabbatar dorewar kashe kudade.”

Shugabar Hukumar Lyn Mengich ta ce an yanke hukuncin dakatar da shirin karin albashin ne bayan tattaunawa da neman shawarwarin jama’a.

Hukumar ta SRC ta fitar da wata sanarwa a hukumance a jaridar Gwamnatin Kenya a watan Agustan 2023 inda ta bayyana shirinta na ƙara albashin ‘yan siyasa masu rike da madafun iko daga 1 ga Yulin 2024.

‘Mu rayu daidai gwargwadon arzikinmu’

Shugaban Kasar Kenya William Ruto ya umarci Ma’aikatar Kudi ta kasa da ta dakatar da shirin karin albashin.

Shugaba Ruto ya ce wannan mataki zai taimaka wa Kenya ‘Ta rayu daidai gwagwardon arzikinta”.

Kungiyar gwamnoni, wadda ta kunshi dukkan gwamnoni 47 na kasar Kenya, ta yi kira ga Hukumar SRC da ta dakatar da shirin karin albashin ‘yan siyasa masu rike da madafun iko.

Sabon tsarin albashin da aka kawo ya tanadi cewa dan majalisar dokoki zai dinga karbar kudin Kenya 739,600 kwatankwancin dalar Amurka 5,730 a kowanne wata, kari kan ksh 725,500 kwatankwacin dala 5,620 da suke karba a halin yanzu.

Almubazzaranci a gwamnati

Sabon albashin gwamnoni zai kama ksh 990,000 ($7,620), daga 957,000 ($7,420) da suke karba a yanzu.

Ministoci kuma da suke da matsayi iri daya da na gwamnonin za su samu kari kwatankwacin na gwamnonin.

Kenya na da ministoci 22.

Karin albashin zai janyo kenya ta kashe kusan Sulallan kasar biliyan 11 (dala miliyan $85.3) a kowacce shekara, kamar yadda jaridar ƙasa ta Kenya ta rawaito a ranar Laraba.

Matakin janye karin albashin ‘yan siyasar ya zo ne a lokacin da ‘yan kasar ke kira ga gwamnatin Ruto da ta kawo karshen almubazzaranci a cikin gwamnati.

Zanga-angar adawa da karin haraji da aka yi a baya-bayan nan a Kenya ta janyo asarar rayukan mutum 39, kamar yadda Hukumar Kare Hakkokin Dan’adam ta Kenya mallakin gwamnati ta sanar.

Zanga-zangar ta sanya Ruto janye Dokar Kudade ta 2024, wadda ta tanadi kara yawan haraji a kasar.

People are also reading