Home Back

Da Ɗuminsa: An Rufe Ƙofa Tsakanin Ƙungiyar Ƙwadago Da Sakataren Gwamnatin Tarayya

leadership.ng 2024/6/26
Biyan Albashin Da Ƙungiyar Ƙwadago Ke Nema Na Iya Durƙusar Da Nijeriya

A wani gagarumin yunƙurin warware yajin aikin da aka tsunduma a fadin kasar, sakataren gwamnatin tarayya George Akume na yin wata ganawar sirri da shugabannin ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC da kuma TUC. Yajin aikin wanda ya fara a yau 3 ga watan Yuni ya biyo bayan gazawar gwamnatin tarayya na kammala tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi da kuma sauya ƙarin kuɗin wutar lantarki da aka yi a baya-bayan nan.

Shugabannin ƙungiyoyin kwadagon da suka haɗa da shugaban NLC, Joe Ajaero da shugaban TUC Festus Osifo, sun bayyana matukar bacin ransu kan yadda gwamnati ke tafiyar da lamarin, musamman rashin halartar gwamnonin jihohi da wakilan tarayya da ke da hurumin yin alkawurra. Sun yi nuni da yadda gwamnati ta ƙi biyan buƙatunsu da kuma rashin taka rawar gani wajen magance matsalolin ma’aikatan.

Ƙungiyoyin ƙwadagon sun fitar da wa’adin ƙarshe na neman a kammala tattaunawar mafi ƙarancin albashi tare da sauya farashin wutar lantarki. Sun yi kira ga abokan hulɗarsu, da majalisun jihohi, da ƙungiyoyin farar hula, da sauran jama’a da su shirya tsaf domin daukar kwararan matakai, tare da jaddada cewa batun jin daɗi da walwalar ma’aikatan Najeriya ba gudu ba ja da baya.

People are also reading