Home Back

Tsagin NNPP Ya Ƙaryata Kwankwaso, Ya Faɗi Masu Kunno Wutar Rikicin Sarautar Kano

legit.ng 2024/7/3
  • Tsagin jam'iyyar NNPP karkashin jagorancin Boniface Aniebonam ya caccaki nesanta kansa da kalaman Kwankwaso kan rigimar sarautar Kano
  • Da yake zantawada manema labarai a Legas, Aniebonam ya ce NNPP ba ta da alaƙa da zargin gwamnatin tarayya ke rura wutar rikicin Kano
  • Ya jaddada cewa tsagin NNPP ya kori Kwankwaso tuntuni saboda haka ba ruwan jam'iyyar da kalaman da ya yi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Jagoran tsagin New Nigeria Peoples Party (NNPP), Dokta Boniface Aniebonam ya nesanta jam'iyyat da kalaman Rabiu Musa Kwankwaso.

Boniface ya ce jam'iyyar NNPP ba ta da alaƙa da zargin da Kwankwaso ya yi cewa gwamnatin tarayya ce take rura wutar rikicin sarauyar da ke faruwa a Kano.

Rabiu Kwankwaso.
Tsagin Aniebonam a NNPP ya nesanta kansa daga ikirarin da Kwankwaso ya yi Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso Asali: Facebook

Ya yi wannan furucin ne yayin zantawa da manema labarai kan danbarwar Kano a jihar Legas ranar Alhamis, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan zaku iya tunawa Kwankwaso ya yi zargin cewa jami'an tsaron da ke alhakin tabbatar da zaman lafiya, sun fake da umarnin kotu suna kare Sarki na 15, Aminu Ado Bayero.

Haka nan kuma Kwankwaso ya zargi gwamnatin tarayya ƙarƙashin Bola Tinubu da APC mai mulki da yunƙurin kirkiro sabuwar kungiyar Boko Haram ta zamani.

Tsagin NNPP ya musanta kalaman Kwankwaso

Da yake martani kan ikirarin Kwankwaso, Mista Aniebonam ya ce tsagin NNPP da yake jagoranta ba ya tare da waɗannan zarge-zarge.

A cewarsa, matsayar jam'iyyar NNPP ta ƙasa game da rigimar sarautar Kano ita ce lamari ne da ya shafi siyasar cikin gida a jihar Kano.

Ya ƙara da cewa irin wannan zargi mai nauyi mara tushe da aka ɗorawa gwamnatin tarayya abin Allah wadai ne domin yana iya tayar da hargitsi a jihar.

"Mun jima da korar Kwankwaso daga tsagin jam'iyyarmi, saboda haka duk kalaman da ya faɗa ba shi da alaƙa da NNPP ta ɓangaren mu."
"Muna da yakinin cewa Gwamnatin Tarayya za ta iya shiga taakani ta sasanta lamarin idan har ta fahimci za a kai ga asarar rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Kano.
"Amma yin irin wannan zargi ba tare da hujja ba ya cikin aƙidarmu, kuma daidai yake da tsokano rigima wanda bamu yarda da haka ba," in ji Aniebonam.

A wani rahoton kuma Babbar kotun tarayya ta yanke hukunci kan dambarwar masarautar Kano tun bayan rushe masarautun jihar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.

Mai shari'a Abdullahi Muhammad Liman a hukuncin da ya zartar a yau ya soke dokar da ta rushe masarautun Kano, sannan ya yi umarnin kowa ya tsaya a matsayinsa.

Asali: Legit.ng

People are also reading