Home Back

An Samu Asarar Rayuka a Bauchi Bayan Barkewar Ruwan Sama Kamar da Bakin Kwarya

legit.ng 2024/7/1
  • An samu ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a jihar Bauchi a ranar Asabar da daddare wanda ya yi sanadiyyar rasuwar mutum biyar
  • Ƴan kasuwan da suka rasu suna a wajen bikin baje kolin kasuwanci ne karo na 15 na shiyyar Arewa maso Gabas da aka shirya a jihar Bauchi
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin a cikin wata sanarwa da kakakinta ya fitar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Aƙalla ƴan kasuwa mutum biyar ne suka mutu sakamakon ruwan sama a wajen bikin baje kolin kasuwanci na haɗin gwiwa na shiyyar Arewa maso Gabas karo na 15 a jihar Bauchi.

Ruwan saman kamar da bakin ƙwarya ya fara ne da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar Asabar, inda ya yi ɓarna a rumfunan kasuwar.

'Yan kasuwa sun rasu a Bauchi
Ruwan sama ya yi sanadiyyar rasuwar 'yan kasuwa a Bauchi Hoto: Bala Mohammed Asali: Twitter

Mutum biyu ne suka mutu nan take bayan rumfuna sun faɗo musu a kasuwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An samu asarar rayuka a Bauchi

An bayyana cewa wasu mutum biyar sun samu raunuka daban-daban da suka haɗa da karaya, sannan an kai su asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa.

Majiyar asibitin ta shaidawa jaridar Daily Trust cewa mutum biyar ne suka mutu yayin da wasu mutum uku ke karɓar magani.

"Mun samu mutanen da suka jikkata da dama daga wurin da lamarin ya faru, abin takaici an kawo biyu matattu, uku kuma sun samu munanan raunuka daga kai har zuwa ciki kuma sun mutu jim kaɗan bayan an kawo su."
"A halin yanzu muna da marasa lafiya mutum uku waɗanda suka samu karaya da yawa da ke karɓar magani kuma sannu a hankali suna samun sauƙi."

- Wata majiya

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta bakin kakakinta SP Ahmed Wakil ta tabbatar da faruwar lamarin.

Ya bayyana cewa rumfunan da suke a tantunan Gombe da Yobe sun faɗo ne a kan mutum biyar inda nan da nan aka garzaya da su zuwa asibiti.

Ya ƙara da cewa mutum huɗu ne suka rasa rayukansu yayin da wata mata mai suna Fatima Isa ke ci gaba da karɓar magani saboda raunin da ta samu.

Ƴan sanda sun cafke magidanci a Bauchi

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta cafke wani magidanci bisa zarginsa da yunƙurin siyar da ɗiyarsa.

Magidancin mai shekara 49 a duniya ya shiga hannu ne bayan an ritsa shi yana yunƙurin siyar da yarinyar mai shekara biyar da haihuwa kan kuɗi N1.5m.

Asali: Legit.ng

People are also reading