Home Back

Kano: An Karrama Yaro Dan Shekara 16 da Kujerar Hajji Saboda Kur’ani

legit.ng 2024/5/7
  • An karrama yaron da ya nuna hazaka a kan hadda da sanin ma'amonin Alkur'ani a jihar Kano da kujerar Hajji
  • Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ce ta bayyana kyautar tare da bayyana dalilai da suka sa aka karrama shi
  • Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ji jawabi mai ratsa zuciyia kan bajintar da yaron ya nuna

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Yaro dan shekara 16 a jihar Kano mai suna Ja'afar Yusuf ya samu damar zuwa aikin Hajjin bana saboda kwarewa a karatun Alkur'ani.

Rahotanni sun nuna cewa an karrama yaron ne saboda haddar Alkur'ani cikakkiya da yake da ita tare da sanin ma'amoninsa.

Kano state government
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce dole a cigaba da karfafan yara irinsa. Hoto: Kano State Pilgrims Welfare Board Asali: Facebook

Hukumar jin dadin aljazai ta jihar ta wallafa a shafinta na Facebook cewa gwamnatin jihar ne ta karrama shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin karrama yaron

A lokacin da yake bayyana kyautar, darakta a hukumar jin dadin alhazai ta jihar, Alhaji Laminu Danbappa, ya ce yaron ya nuna bajinta sosai.

A cewarsa hukumar ta ba wa yaron kyautar ne saboda kwarewarsa a fannin karatun Alkur'ani abin a yaba ne matuka

Ya kara da cewa yaron ya fahimci dukkan ma'amonin kalmomin Alkur'ani tare da sanin a surar da kowace kalma ta take.

Jawabin gwamnan jihar Kano

A cewar jami'in yada labarai na hukumar, Sulaiman Dederi, gwaman jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da kansa ya yabawa yaron ya kuma ce ya zamo abin misali ga sauran al'umma.

A cewar gwamnan, hazakar da yaron ya nuna tana bayyana irin jajircewa da lura da addini da aka san mutanen Kano da ita.

Sannan ya kara da cewa akwai muhimmanci sosai wurin karfafawa yara masu hazaka gwiwa domin samar da manyan gobe masu nagarta.

Gwamnatin jihar Kano ta tallafawa alhazai

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da bayar da tallafin N500,000 ga kowane maniyyacin aikin hajjin 2024 a jihar

Gwamna Yusuf ya ce tallafin N500,000 zai shafi wadanda suka biya Naira miliyan 4.9 na farko kuma aka bukaci su biya karin Naira miliyan 1.9

Asali: Legit.ng

People are also reading