Home Back

Salah ya yi ta'aziya ga iyalan Refaat ɗan ƙwallon masar da ya rasu

bbc.com 2024/7/7
Ahmed Refaat

Asalin hoton, Getty Images

Mohamed Salah ya yi ta'aziyar rasuwar ɗan wasan Masar, Ahmed Refaat, wanda ya mutu sakamakon bugun zuciya, bayan da ya fadi a fili ana tsaka da wasa.

Ɗan ƙwallon ya rasu yana da shekara 31 ranar Asabar da sanyin safiya, bayan da ya yi fama da bugun zuciya.

Refaat ya wakilci tawagar Masar a manyan wasannin tamaula tare da kyaftin ɗin tawagar, Salah wanda ya yi ta'aziyar a kafarsa ta sada zumunta.

Lamarin ya faru ne a lokacin lik a gasar Masar a wasa tsakanin Modern Furure da Al Ittihad Alexandria, wanda ya faɗi a filin, daga nan aka garzaya da shi asibiti.

Daga lokacin aka sawa ɗan wasan na'urar da take taimakawa mara lafiya yin numfashi, wanda ya yi kwana tara bai san inda yake ba.

Refaat bai farfaɗo ba daga wannan lokacin, inda ƙungiyarsa ta bayar da rahoton mutuwar ɗan ƙwallon.

Refaat - wanda ya ci ƙwallo biyu a wasa bakwai a Masar tsakanin 2013 zuwa 20222 ya taɓa faduwa a fili ana tsaka da wasa a cikin watan Maris.

Ya wakilci tawagar ƙwallon kafa ta Masar ta matasa da ta babbar kasar da ya buga wa wasa bakwai ɗaya daga ciki ya taka leda tare da Salah na Liverpool.

Salah ya wallafa a shafinsa na X cewa: 'Rayuwa ta Allah ce, kuma Allah ya ba iyalansa da dukkan masoyansa hakuri.

Kauce wa Twitter
Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a Twitter

Refaat, wanda ke taka leda daga gefen gaba ya buga wa ENPPI SC da Al Ittihad Alexandria da Zamalek da Al Masry a Masar da kuma Al Wahda a haɗaɗiyar daulal Larabawa, wato UAE.

Yana cikin tawagar Masar da ta lashe kofin Afirka na ƴan kasa da shekara 20 a 2013 daga nan ya ɗauki Egyptian Super Cup da Zamalek a 2017 da kuma Egyptian League Cup da Modern Future a 2022.

People are also reading