Home Back

Kenya ta tsuke bakin aljihu

dw.com 3 days ago
Masu zanga-zanga a birnin Nairobi na Kenya
Masu zanga-zanga a Kenya

Gwamnatin Kenya ta tabbatar da daukan matakan tsuke bakin aljihu bayan zanga-zangar matasa da ta janyo soke kudirin dokar kasafin kudi mai cike da rudani. Minsitan kudin kasar Njuguna Ndung'u ya ce gwamnati ta dauki matakin zaftare kudin da kashewa, saboda watsi da ayar dokar da ta tanaji samun kudin shiga na haraji kimanin dalar Amirka milyan dubu biyu da digo bakwai.

A makon jiya Shugaba William Ruto na kasar ta Kenya ya janye dokar samakon matsin lambar masu zanga-zanga. Ita dai kasar Kenya tana neman hanyar samun kudin shiga sakamakon yadda bashi ya kawo mata har wuya.

Sai dai gwamnatin ta ce tana shirya da duba wasu hanyoyin domin samun kudin shiga. Kimanin mutane 30 aka tabbatar sun mutu sakamakon zanga-zangar adawa da kudirin dakar harajin da gwamnatin ta janye saboda fusata da mutane suka nuna.

People are also reading