Home Back

LP ba jam’iyya ba ce, ƙungiyar asiri ce – Kenneth Okonkwo bayan ya fice

premiumtimesng.com 2024/7/4
LP ba jam’iyya ba ce, ƙungiyar asiri ce – Kenneth Okonkwo bayan ya fice

Fitaccen ɗan fim wanda ya koma ɗan siyasa, Kenneth Okonkwo, ya ragargaji jam’iyyar LP, wadda Peter Obi ya yi takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin ta.

Okonkwo wanda ya koma LP a ranar 24 ga Agusta, 2022, wata bayan fita daga APC, ya ce LP ba jam’iyyar siyasa ba ce gungun ‘yan ƙungiyar asiri ce.

Okonkwo ya fice daga APC saboda bai gamsu da yadda jam’iyyar ta tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa da na mataimakin sa duk Musulmai, wato Muslim-Muslim Ticket’.

A wancan lokacin, ya ce ya shiga LP domin samar da nagartacciyar gwamnati.

Sai dai kuma a wata tattaunawa da aka yi dai a ‘Symfoni TV’, aka watsa a YouTube, a ranar 15 Ga Yuni, Okonkwo wanda ya riƙe muƙamin Kakakin Yaɗa Labarai na kamfen ɗin ɗan takarar yaƙin neman zaɓen ƙasa, LP ta kauce hanyar da aka gina ta tun da farko.

Okonkwo ya yi wannan kakkausan zargin kan Shugaban Jam’iyyar LP na ƙasa, Julius Abure da sauran shugabannin LP.

Ya yi wannan bayani dangane da taron gangamin da LP ɗin ta gudanar a cikin watan Maris, a Jihar Anambra, wanda Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi fatali da shi.

“Ba Ni ma da masaniyar cewa LP ta yi taron kwanbenshin, kuma na gode Ubangiji kai ma ɗan jarida ba su bari ka shiga ba. Saboda ba a son ‘yan jarida su bankaɗo gaskiyar abin da suke ciki a wurin taron. Sai suka hana ‘yan jarida shiga.

“Wannan ƙungiyar asiri ce, ba jam’iyyar siyasa. Kamata ya yi a kama su domin su yi bayanin abin da suka ƙulla a asirce. Harkokin siyasa abu ne na fili ba nuƙu-nuƙu. Saboda haka Julius Abure da ‘yan jagaliyar sa su fito su yi mana jawabin abin da suka yi asirce.”

People are also reading