Home Back

'Yan Nijar sun yi zanga-zanga neman ficewar sojojin Amurka

dw.com 2024/5/16
Niger Protest gegen die US-Militärpräsenz in Niamey
Hoto: Mahamadou Hamidou/REUTERS

Kwanaki kalilan bayan da gwamnatin mulkin sojin Nijar ta yi Allah wadai da yarjejeniyar tsaro da ke tsakanin Nijar da Amurka, dubban 'yan kasar sun fito a ranar Asabar 13.04.2024 inda suka gudanar da gagarumar zanga-zanga suna masu bukatar sojojin Amurka su gaggauta ficewa.

Masu aiko da rohotanni sun ce zanga-zangar da kungiyoyi fararen hula da na addini Musulunci sama da guda 10 suka kira ta samu karbuwa, inda dubban mahalarta dauke da tutocin Nijar da Mali da Burkina Faso da kuma Rasha suka yi ta daga alluna masu dauke da rubutun batanci ga tsarin jari hujja na kasashen Yammacin duniya.

Wannan gangami na zuwa ne kwanaki uku bayan da wata tawagar sojojin Rasha kusan su 100 ta isa Nijar tare da kayan yaki na zamani da nufin horas da sojojin kasar dabarun yaki, a karkashin sabuwar huldar diflomasiyya da mahukuntan soji na Yamai suka kulla da Moscow.

Akalla sojojin Amurka 1,000 ne dai ke jibge a Nijar a wani sansani da ke birnin Agadez a Arewacin kasar, kuma a cewar hukuomin sojin Nijar din Washington ta yi alkawarin gabatar da jaddawali na tattare komatsenta domin ficewa daga kasar sai dai amma ba ta yi ba wani haske ba a kai.

People are also reading