Home Back

SABABIN ƳAN BINDIGA: Masu garkuwa da mahaifiyar Rarara na neman Naira miliyan 900 kuɗin fansar ta

premiumtimesng.com 4 days ago
Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar Rarara, kwana biyu bayan taron Gwamnonin Arewa maso Yamma kan tsaro a Katsina

Waɗanda suka yi garkuwa da mahaifiyar mawaƙi Dauda Kahutu Rarara, sun nemi a biya su kuɗin fansa har Naira miliyan 900 kafin su sake ta.

Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai sun tabbatar da cewa majiya ce daga iyalan Hajiya Hauwa’u a ƙauyen Kahutu suka tabbatar da hakan, amma kuma nahiyar Turai a nemi a ɓoye sunan sa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa waɗanda suka sace mahaifiyar fitaccen mawaƙin sun kira iyalan gidan, inda da farko suka nemi a biya su Naira biliyan 1.

“Sun kira iyalan gyatumar da wata wayar da suka ƙwace daga hannun wata mata a lokacin da suka shiga cikin gidan suka tafi da Hajiya.

“Sun nemi a biya su Naira biliyan 1, amma bayan an yi ‘yar tattaunawa da su, sai suka rage kuɗin zuwa Naira miliyan 900.

“Da farko da Rarara suka so yin jingar abin da za a biya su. Amma saboda Rarara ba shi da lafiya tun bayan sace mahaifiyar ta sa, sai suka yi magana da ɗaya daga cikin iyalin su.

“Masu garkuwar sun tabbatar masu Hajiya na cikin ƙoshin lafiya, za su sake ta nan da nan da an haɗa masu Naira miliyan 900 sun shiga hannun su.

“Maganar da aka yi da su ba mai tsawo ba ce. Kuma daga nan ba su ƙara kira ba. Amma dai na tabbatar ana ci gaba da tattaunawar. Yanzu iyalan mahaifiyar Rarara na jiran masu riƙe da ita ɗin su sake kira domin a ci gaba da tattaunawa.”

Yadda ‘Yan Bindiga Suka Gane Mahaifiyar Rarara:

Majiyar Daily Trust ta ce maharan sun je da hoton ta riƙe a hannun su, don gudun kada su kama wadda ba ita ce ba.

“Mun ji cewa lokacin da suka shiga cikin ɗakin ta, sun tashi dukkan matan da ke barci tare da ita a cikin ɗakin, su na kallon su tare ɗaya bayan ɗaya, su na kwatantawa da fuskar hoton da ke hannun su.

“Bayan sun tabbatar cewa sun gane mahaifiyar Rarara, sai suka ce a ba su kuɗi. Aka nuna masu kuɗi a cikin aljihun gefen gadon ta, wato ‘bedside drawer’, amma sai suka ce kuɗin ai cikin cokali ne.

“A ƙarshe suka ce to za su tafi da ita. Gyatumar ba ta yi masu gardama ba, ta tashi suka yi gaba da ita.”

Tuni dai ƙauyen Kahutu da ke cikin Ƙaramar Hukumar Ɗanja a Jihar Katsina ya afka cikin ruɗani, tun bayan garkuwa da mahaifiyar Rarara.

Har yau tun da Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Katsina, Aliyu Abubakar Sadiq ya ce an kama mutum da ake zargi da hannu, ba a ƙara jin wani ƙarin bayani daga bakin sa ba.

People are also reading