Home Back

Yahaya Bello: Kotu Ta Umarci Shugaban EFCC Ya Gurfana a Gabanta, Ta Jero Dalilai

legit.ng 2024/5/12
  • Yayin da ake cece-kuce game da tuhumar da ake kan tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, kotu ta ba da sabon umarni
  • Babbar kotun jihar da ke zamanta a birnin Lokoja ta umarci shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya hallara a gabanta
  • Kotun ta dauki wannan mataki ne kan zargin shugaban hukumar da saba umarnin da ta bayar kan binciken Yahaya Bello

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi - Babbar kotun jihar Kogi ta ba da umarni ga shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya gurfana a gabanta.

Kotun ta umarci shugaban hukumar ya tabbatar ya amsa kira zuwa ranar 13 ga watan Mayun 2023 kan saɓa umarninta.

Shugaban hukumar na fuskantar tuhume-tuhume kan zargin ci gaba da ɗaukar wasu matakai bayan umarnin kotun, cewar Channels TV.

Yayin ba da umarnin, alkalin kotun, Mai Shari'a, I. A Jamil ya de hukumar ta saba dokar da aka gindaya mata wurin aiwatar da wasu ayyuka kan binciken Yahaya Bello.

Alkalin kotun ya yi hukuncin ne kan korafin da lauyan Yahaya Bello, M. S Yusuf ya shigar kan saɓa doka da hukumar ta yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jamil ya umarci shugaban hukumar ya hallara a gabanta domin amsa tambayoyi kan zargin saɓa umarninta.

Wannan na zuwa ne bayan hukumar ta yi wa gidan tsohon gwamnan ƙawanya kan zargin badakalar N84bn lokacin da ya ke mulki.

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading