Home Back

Sojojin Sama Sun Yi Lugudan Wuta Kan Ƴan Ta’adda A Kaduna

leadership.ng 2024/8/23
Sojojin Sama Sun Yi Lugudan Wuta Kan Ƴan Ta’adda A Kaduna

Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) ta sanar da cewa ɓangaren Sojojin sama na Operation Whirl Stroke sun kai hare-hare ta sama wanda ya hallaka ‘yan ta’adda da dama a maɓoyarsu da ke ƙananan Hukumomin Giwa da Igabi na Jihar Kaduna.

A cewar wata sanarwa da AVM Edward Gabkwet, Daraktan hulɗa da Jama’a ya fitar, ana ci gaba da samun nasara a waɗannan hare-haren duk da matsalolin yanayi da ke addabar yankin Arewa maso Yamma.

Ɗaya daga cikin hare-haren da aka kai shi ne a ranar Juma’a a maɓoyar Alhaji Layi dake ƙauyen Kufan Shantu, ƙaramar hukumar Giwa, inda aka lalata kayan aiki da ‘yan ta’addan suka ɓoya a ƙarƙashin bishiyoyi.

An samu nasarar kai wani hari a ranar Asabar a sansanin ‘yan ta’adda a cikin dajin Malum da ke ƙaramar hukumar Igabi. Harin dai an kai shi ne bayan samun cikakkun kwararan bayanan sirri, tare da gudanar da lissafi da leken asiri, ya kashe mafi yawan ‘yan ta’addan da aka gani suna yawo a cikin dajin.

Waɗannan hare-haren ta sama an yi su ne sakamakon bayanan sirri da suka nuna wuraren da aka nufa a matsayin maboyar ‘yan ta’addan da suka kai hari kan sojoji a Manini a ranar 10 ga Yuli.

AVM Gabkwet ya jaddada cewa NAF, tare da haɗin gwuiwar Sojojin ƙasa, za su ci gaba da samun rinjaye ta hanyar lura da yanayi, da gudanar da sintiri akai-akai, da kuma kai hare-hare kai tsaye kan maɓoyar ‘yan ta’adda. Wannan dabarar na nufin kawar da ta’addanci da sauran laifuka a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

People are also reading