Tinubu Ya Kashe N814bn Domin Sauya Taken Kasa? Gaskiya Ta Bayyana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rattaɓa hannu kan ƙudirin dokar sauya taken ƙasa daga "Arise O Compatriots" zuwa "Nigeria We Hail Thee" a ranar 29 ga watan Mayun 2024.
Wasu ƴan Najeriya sun yabawa shugaban ƙasan kan wannan matakin yayin da wasu da dama suka yi Allah wadai da hakan.
Masu adawa da sauyin da aka yiwa taken ƙasan sun nuna rashin muhimmancin yin sauyin a halin yanzu duba da halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani shafin yanar gizo na RWGblog ya yi iƙirarin cewa gwamnatin tarayya ta laƙume N814bn wajen sauya taken ƙasan.
Shafin ya yi iƙirarin cewa ministan kasafin kuɗi, Atiku Bagudu ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.
Rubutun da shafin ya yi dai ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta musamman Facebook da X (wanda a baya aka fi sani da Twitter).
An sake wallafa rubutun a nan, nan, nan, nan da nan.
Sai dai, shafin Dubawa mai binciken gaskiya, ya binciki shafin ministan na Facebook kuma bai samu inda Atiku Bagudu ya bayyana cewa an kashe waɗannan kuɗaɗen ba.
Haka kuma, shafukan sada zumunta na ma'aikatar kasafin kuɗi ba su wallafa cewa an kashe kuɗaɗen ba.
Daga nan sai aka tuntuɓi mataimaki na musamman kan yaɗa labarai na Atiku Bagudu, Bolaji Adeniyi, domin samun ƙarin bayani.
Ya bayyana cewa ministan bai taɓa yin wata magana ba a kan sabon taken ƙasan da aka dawo da shi ba.
"Mun yi magana kan wannan batun a kwanakin baya. Ministan bai taɓa yin magana a kan sabon taken ƙasan ba."
"Ba ya da masaniya cewa an yi wani kasafin kuɗi domin sabon taken ƙasan. Wannan labarin ƙarya ne."
- Bolaji Adeniyi
Haka kuma a cikin wani rahoton jaridar The Cable, Lanre Issa-Onilu, shugaban hukumar wayar da kai ta ƙasa (NOA), ya ce hukumar ba ta karɓi wasu kuɗi ba domin sabon taken ƙasan.
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawa ta tabbatar da ƙudirin dawo da tsohon taken Najeriya wanda aka daina amfani da shi domin ƙara kishin ƙasa.
Majalisar dattawan ta amince da ƙudirin sauya taken ƙasan ne bayan ya tsallake karatu na 3 a ranar Talata 28 ga watan Mayun 2024.
Asali: Legit.ng