Home Back

An Wallafa Makalar Da Xi Jinping Ya Rubuta Mai Taken “Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Kazakhstan Cikin Hadin Kai”

leadership.ng 3 days ago
An Wallafa Makalar Da Xi Jinping Ya Rubuta Mai Taken “Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Kazakhstan Cikin Hadin Kai”

An wallafa makalar da Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubuta mai taken “Bude sabon babin huldar Sin da Kazakhstan cikin hadin kai” a jaridar “Kazakhstanskaya Pravda” da kamfanin dillancin labarai na kasa da kasa na Kazakhstan a yau Talata yayin da yake ziyarar aiki a kasar. A cikin makalarsa, ya bayyana fatansa na hadin kai da takwaransa na kasar Kassym-Jomart Kemeluly Tokayev a ziyararsa na wannan karo, don habaka dankon zumuncin kasashen biyu da zurfafa hadin gwiwarsu a dukkanin fannoni, da ma gabatar da sabbin tsare-tsaren raya huldar kasashen biyu nan gaba, kana da ingiza dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare a duk fanonni tsakaninsu zuwa wani sabon mataki.

Wannan ziyara ta kasance karo na 5 da shugaba Xi Jinping ya yi a kasar Kazakhsatan a wa’adinsa.

Wani muhimmin aiki na daban a ziyarar Xi Jinping a wannan karo shi ne halartar taron koli na kungiyar hadin kai ta Shanghai. Ya yi imani cewa, ba shakka za a cimma nasara a taron da za a gudanar a Astana, fadar mulkin kasar karkashin kokarin bangarori daban-daban, da ma habaka zumuncin mambobin kungiyar, ta yadda za a bude wani sabon babin hadin gwiwarsu. (Amina Xu)

People are also reading