Home Back

Ku Riƙa Bincike Kafin Ku Yi Magana, Martanin Gwamnatin Katsina Ga ASUU

leadership.ng 3 days ago
Ku Riƙa Bincike Kafin Ku Yi Magana, Martanin Gwamnatin Katsina Ga ASUU

Gwamnatin jihar Katsina ta mayar wa ƙungiyar Malaman jami’a ASUU reshen jami’ar Yar’adua da ke Katsina martani dangane da iƙirarin da ƙungiyar ta yi na cewa jami’ar ta kama hanyar durƙushewa. 

Kwamishinan ma’aikatan ilimi mai zurfi da kula da ƙere-ƙere Ferfasa Abdulhamid Ahmad ya maida martanin ne da cewa ba gwamnatin su ba ce ta rage kuɗaɗen gudanarwar jami’ar ba.

Wannan gwamnatin ƙarkashin jagorancin Malam Dikko Umar Raɗɗa bata taɓa rage ko Naira ba daga kuɗaɗen gudanarwa da ake ba jami’ar Yar’adua kuma ba a taɓa fashin biyan su ba.”inji shi.

Kwamishinan wanda ya ce shi daya ne daga cikin Malaman jami’ar kafin ya samu muƙami yasan duk abinda ke faruwa yana da masaniyar musamman tafiyar da sha’anin jami’ar

Kazalika ya yi kira ga ƙungiyar ASUU da ta koma jami’ar ta bincika ta gani daga yaushe ne aka rage waɗancan kuɗaɗen da suke magana, ba wai su fito a kafafen yaɗa labarai suna faɗin abinda ba haka yake ba.

Sannan ya ƙara da cewa babu wanda ya taɓa rubutawa gwamnati cewa kuɗaɗen gudanarwa da ake ba jami’ar da sauran manyan makarantu ba sa isar su, babu wanda ya taɓa sanar da gwamnati.

“Kuma ina san jama’a da su gane, ASUU sun ce adadin ɗalibai da tsangaya sun ƙaro, to su bayyanawa duniya adadin kuɗaɗen shiga da suke samu a yanzu kowa ya sani.

A cewar sa, ko Naira ɗaya basa ba gwamnatin jihar Katsina, su ke tara kuɗin su, su ke kashe su, saboda haka ya ce su je su bincika tun shekarar 2015 aka fara zabtare kuɗaɗen gudanarwa na jami’ar da sauran makarantu guda biyar.

Da kwamishinan ya juya game da korafin da ƙungiyar ASUU ta yi na cewa gwamnatin tarayya ta fara aiwatar da shirin ƙarin albashi na kaso 25/35 ya ce yanzu haka maganar tana kan teburin gwamna Dikko Umar Raɗɗa jira ake akwai ya bada umarni.

Ya ƙara da cewa maganar ƙarin albashi da ƙungiyar ƙwadago ya bijiro da shi, ya tsayar da batun, amma tuni an gama wannan maganar, yana mai cewa ya sanar da duk manyan makarantun da suke ƙarƙashin kulawar ma’aikatarsa, inda aka kwana da inda aka tashi akan batun ƙarin albashi, amma ba wai an fasa ba.

Ferfasa Abdulhamid Ahmad ya ce akwai abubuwa da yawa da gwamnatin jihar Katsina ta shirya yi ɓangaren ilimi wanda ya ce wasu ba zai faɗe su ba yanzu, sai nan gaba saboda mahimmancin su ga jihar Katsina.

Ya kuma ƙalubalanci jami’ar Yar’adua wanda ya ce gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ya yi alkawarin cewa duk dalibin da ya fita da digiri mai daraja ta farko zai ɗauke aiki ba tare da ɓata lokaci ba, amma ya ce kusan wata biyu da yin wannan batu har gobe jami’ar bata rubutu a rubuce ba tana san a aiwatar da wancan alƙawari.

People are also reading