Home Back

Ana Tsakar Tattaunawa, Tsohon Ƙusa a APC ya Zuga NLC kan Mafi Karancin Albashi

legit.ng 2024/7/6
  • Tsohon mataimakin sakataren yaɗa labarai a jam'iyyar APC, Timi Frank ya shawarci ƙungiyoyin ƙwadago da ka da su saurara kan batun mafi ƙarancin albashi
  • Jigo a jam'iyya mai mulki ya bayar da shawarar ne lokacin da ake tsaka da tattaunawa tsakanin kwamitin gwamnati da kungiyoyin ƙwadago kan bayyana matsayar da aka cimma
  • Timi Frank ya ce bai ga dalilin da zai sa gwamnati ta yi ƙarin 300% ga ma'aikatan ɓangren shari'a ba amma ta gaza yin wani abin arziƙi ga talakawa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Abuja- Tsohon mataimakin sakataren yaɗa labaran jam'iyyar APC na ƙasa, Timi Frank ya shawarci kungiyar ƙwadago ta NLC kan mafi ƙarancin albashi. Shawarar ta sa na zuwa a dai-dai gaɓar da ƙungiyoyin ƙwadago da gwamnati su ke ganawa kan bayyana mafi ƙarancin albashin.

Kwadago
Jigo a APC, Timi Frank ya buƙaci ƙungiyoyin ƙwadago ka da su karɓi tayin kasa da ₦250,000 Hoto: @RealTimiFrank, @NLCHeadquarters Asali: Twitter

Leadership News ta tattaro cewa tsohon sakataren yaɗa labaran na ganin kada NLC ta karɓi ƙasa da ₦250,000. Ana dai ta raɗe-raɗin ₦105,000 gwamnatin tarayya ta amince za ta iya biyan ma'aikatan ƙasar, amma hadimin shugaban ƙasa, Wale Onanuga ya musanta batun.

"Gwamnatin Tinubu na son kai," Frank

Tsohon sakataren yaɗa labarai a jam'iyyar APC, Timi Frank ya zargi gwamnatinsu da fuska biyu kan batun mafi ƙarancin albashi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Pulse Nigeria ta wallafa Timi Frank na cewa idan gwamnati za ta iya yin ƙarin 300% ga jami'an ɓangaren shari'a, babu dalilin ƙin yi wa ma'aikata ƙari mai tsoka.

Ya ce yanzu haka ƙudurin fara biyan albashin manya-manyan ma'aikatan ɓangaren shari'a na jiran sa hannun shugaban kasa ne kawai ya zama doka.

Ya shawarci ƙungiyoyin NLC da TUC ka da su sassauta ƙasa da ₦250,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Gwamnati ta musanta tayin sabon albashi

A baya mun kawo muku rahoton cewa gwamnatin tarayya ta musanta cewa ta karɓi lissafin sabon tsarin mafi ƙarancin albashi kamar yadda ake yaɗawa.

Hadimin shugaban kasa kan yaɗa labarai, Wale Onanuga ya ce babu ƙamshin gaskiya kan labarin Ministan kuɗi da tattalin arziƙi, Wale Edun ya miƙa tayin ₦105,000.

Asali: Legit.ng

People are also reading