Home Back

CP Salman: Abin da Muka Sani Game da Sabon Kwamishinan Ƴan Sandan Kano

legit.ng 2024/7/3

Jihar Kano - A ranar Litinin, 24 ga watan Yunin 2024 sabon kwamishinan ƴan sanda da aka tura zuwa jihar Kano, CP Salman Dogo Garba ya kamata aiki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

CP Salman Garba ya karbi ragamar rundunar ƴan sandan ne daga Usaini Gumel wanda aka karawa matsayi zuwa muƙamin mataimakin Sufeta Janar.

Kamar yadda muka ruwaito, CP Salman Garba ya lashi takobin yin aiki tuƙuru domin wanzar da zaman lafiya a Kano da kuma kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar.

Abin da muka sani game da sabon kwamishinan 'yan sandan Kano
CP Salman ya kama aiki matsayin sabon kwamishinan 'yan sandan Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa Asali: Facebook

Abin da muka sani game da CP Salman

Kakakin rundunar ƴan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya zayyana wasu muhimman abubuwa game da rayuwar sabon kwamishinan a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Haihuwar CP Salman da karatu

An haifi CP Salman a ranar 21 ga watan Yulin 1996 a Ilorin ta Yamma da ke jihar Kwara. Ya yi karatun firamare a Al-Mubarak.

Ya yi karatun sakandare a kwalejin malamai ta Kabba, sannan ya garzaya jami'ar Ahmadu Bello, ina ya samu shaidar kammala digirin farko.

2. Shiga aikin ɗan sanda a shekarar 1992

CP Salman ya shiga aikin ɗan sanda a ranar 18 ga watan Mayun 1992 a matsayin C/ASP, kuma ya samu horo a makarantar ƴan sanda ta Kano.

An fara tura shi ofishin ƴan sanda na Garki a shekarar 1994.

3. Muƙaman da CP Salman ya riƙe

Daga shekarar 1995 zuwa 2014, ya rike mukamai da dama ciki har da: DCO, OC/SARS, DPO, SOS, CSP 'A', ACM, da kuma muƙamin AC na ofishin Wudil.

Daga shekarar 2019 zuwa 2024, CP Salman ya samu ƙarin girma zuwa muƙamin DCP (2019-2022); CP (2022-2024).

CP Salman ya yi aiki a jihohin Najeriya da dama ciki har da, Abuja, Delta, Osun, Legas, Kaduna, Anambra, Bauchi, da kuma Kano.

4. Kwasa-kwasan da CP Salman ya halarta

CP Salman ya halarci kwasa-kwasai da dama, ya halarci tarurrukan karawa juna sani, da tarurrukan ba da horo a ciki da wajen Najeriya.

Ya halarci kwas ɗin 'yan sanda a Amurka a 2008, a 1999 na yi kwas a kwalejin 'yan sanda ta Jos, sannan ya yi kwas a makarantar jami'an sojin Najeriya da ke Legas a 2010.

A shekarar 2018 ya sake komawa kwalejin 'yan sanda ta Jos inda ya yi kwana kan sanin makamar shugananci.

Yan sanda sun mamaye fadar sarkin Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa jami'an rundunar 'yan sanda sun fatattaki 'yan tauri da ke gadin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a fadar Rumfa.

Bayan korar 'yan taurin, an ruwaito cewa yan sandan sun mamaye fadar sarkin tare da zama masu tsaron ta, a wani yunkuri da ake zargi na maido da Aminu Bayero fadar.

Asali: Legit.ng

People are also reading