Gwamnatin Najeriya Ta Yi Albishir Kan Aikin Jirgin Kasan Legas Zuwa Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Ministan sufuri, Sanata Sa'idu Ahmed Alkali ya bayyana cewa jirgin kasan Kano zuwa Legas zai fara zirga zirga a yau Alhamis.
Sanata Sa'idu Ahmed Alkali ya bayyana cewa titin jirgin zai dawo aiki ne bayan an masa wasu gyare-gyare.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sanata Alkali ya ce dawo da titin jirgin aiki na cikin kokarin Bola Tinubu na cigaba da ayyukan da ya gada.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan sufuri ya tabbatar da cewa za a samu alfanu sosai saboda dawowar aikin da jirgin kasan zai yi a yau musamman a harkar tattalin arziki.
Ya ce za a samu sauƙin hada-hadar kaya tsakanin Kudu da Arewa musamman ma a yanzu da farashin man fetur ya tashi.
Sanata Alkali ya kara da cewa za a kara samun raguwar haduran da ake a kan titunan Najeriya wanda suke jawo asarar rayuka da dukiya.
A karkashin haka, ya ce ana sa ran samun sauƙin farashin kayan masarufi a kasuwannin Najeriya saboda sauƙin da jirgin kasan zai samar.
Sanata Alkali ya ce karasa gyaran tashar jirgin na daga cikin manyan abubuwan da shugaba Bola Tinubu ya dauka domin inganta sufuri a Najeriya.
Ya kuma kara da cewa idan gwamnatoci masu zuwa za su yi tunanin samar da wasu jiragen kasan da sauran ayyukan cigaba to za a yi nasarar ciyar da Najeriya gaba.
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyoyin kwadagon Najeriya na NLC da TUC sun dakatar da yajin aikin da suke yi a fadin kasar na tsawon mako guda.
Rahotanni sun nuna cewa hakan ya biyo bayan wani taro na musamman da majalisar zartarwar kungiyoyin ta kasa da suka yi a safiyar Talata a Abuja.
Asali: Legit.ng