Home Back

Rasha za ta sanya maza majiya karfi cikin aiki soji.

dw.com 2024/5/18
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin

Matakin daukar dubban mazan na kunshe ne a cikin wata takardar da fadar Kremli ta wallafa a shafinta na Internet. A cewar takadar, dukannin mazan Rasha za su shiga aikin soji na tilas na tsawon shekara guda.

Ko da yake 'yan kasar na kokarin kaucewa shiga aikin sojin, sai dai ma'aikatar tsaron kasar ta tabbatar da cewa ba za a tura sabbin sojoji zuwa filin daga ba a yakin da kasar ke yi da Ukraine; saboda dokar kasar ba ta bayar da damar tura su yaki wajen Rasha ba.

Har wayau, ma'aikatar ta kuma wallafa takardar da ke nuna sojojin da suka kamalla samun horo a matakin farko wanda ta ba su zabin yin aikin sa kai a Ukraine. Ma'aikatar tsaron Birtaniya dai ta yi kirasin cewa, dakarun Rasha 355,000 ne aka kashe tun bayan da kasar ta kaddamar da mamaya a Ukraine a watan Fabarairun shekarar 2022.

People are also reading