Home Back

‘Yan Nijeriya Za Su Sha Wahala Matukar Ba A Biyan Alkalai Albashi – Babban Joji

leadership.ng 2024/6/29
joji

Babban Alkalin-alkalan Nijeriya, Olukayode Ariwoola, ya ce ‘yan Nijeriya za su sha wahala sosai muddin aka kasa biyan alkalai albashi mai kyau da alawus-alawus da sauran hakkokinsu.

Ariwoola ya shaida hakan ne a ranar Litinin yayin jin ba’asin jama’a kan shirin kara albashi da alawus ga ma’aikatan sashin shari’a a Nijeriya.

Jin ba’asin wanda kwamitin majalisar dattawa kan harkokin shari’a da kare hakkin Bil’adama da lamuran shari’a ta shirya.

Ariwoola wanda ya samu wakilcin babban Jojin Jihar Borno, Kashim Zannah, ya ce akwai bukatar karin albashin ga ma’aikatan sashin shari’a domin al’umman kasa ne za a yi wa.

“A lokacin da alkalai suka kasance suna samun hakkokinsu yadda ya dace, tabbas za su ba da himma. Amma idan aka samu akasin haka, to lallai ba za su tsaya su maida hankali wajen kare ra’ayin jama’a ba domin su ma suna cikin yanayi na shan wahala.”

Ya misalta halin da alkalai suke ciki a kasar nan da yanayi kawai da suke bi na hakuri da juriya, inda ya nuna cewa akwai bukatar a dauki matakin gaggawa wajen shawo kan hakan.
“Halin da alkalai ke ciki na yanayin rashin lafiya ne. Idan mai ba da lafiya bai da lafiya kun ga ba zai iya kokarin warkar da wani ba.”

Alkalin-alkalan Nijeriya ya jinjina wa kwamitin majalisar dattawan kan shirya taron jin ba’asin, inda ya nuna hakan a matsayin wani mataki da za a iya bi wajen shawo kan matsalolin albashi da alawus din alkalai.

Shi kuma a jawabinsa, ministan shari’a, Lateef Fagbemi, ya ce yunkurin karin albashi ga ma’aikatan sashin shari’a ya kasa cimma nasara a gwamnatin da ta shude.

Ya nuna kwarin gwiwar cewa gwamnatin tarayya a karkashin Bola Tinubu za ta yi abun da ya dace wajen karin albashi ga ma’aikatan sashin shari’a lura da muhimmancinsu a cikin al’umma.

Ministan kudi, Wale Edun, ya jinjina wa majalisar kasa kan amincewa da karin duba bukatar karin albashin. Sai ya yi kira a gaggauta amincewa da kudurin domin amfanun sashin shari’a da kasa baki daya.

People are also reading