Home Back

Hukumar firimiyar Najeriya ta ci tarar kungiyar kwallon kafa ta Gombe United

rfi.fr 2024/5/5

Hukumar shirya gasar Premier ta Najeriya NPFL ta ci tarar kungiyar kwallon kafa ta Gombe United, tarar maki Uku da Kwallo Uku da ta samu a cikin wanda take da su a baya.

Wallafawa ranar: 22/03/2024 - 14:38Chanzawa ranar: 22/03/2024 - 14:39

Tambarin hukumar shirya gasar league din Najeriya
Tambarin hukumar shirya gasar league din Najeriya © NPFL

Hukumar ta NPFL ta sanar da daukar matakin ne a cikin wata sanarwa da fitar a ranar Alhamis din da ta gabata.

Wannan dai wani mataki ne na ladabtar da kungiyar bayan kin daukar matakan bada kariya ga jami'an da suka jagoranci Alkalancin wasan da ta Fafata na 26, a filin wasa na Pantami tsakaninta da Akwa United wasan da aka tashi Kunnen doki wato 1-1.

Bayan tashi daga wasan dai magoya bayan Gombe United sun farmaki jami'an da suka gudanar da wasan.

People are also reading