Home Back

Karancin Wuta: Majalisar Dokokin Nasarawa Ta Bai Wa AEDC Makonni 2 Don Gyara Wutar Lantarki

leadership.ng 2024/5/17
Karancin Wuta: Majalisar Dokokin Nasarawa Ta Bai Wa AEDC Makonni 2 Don Gyara Wutar Lantarki

Majalisar dokokin Jihar Nasarawa ta bai wa kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distrust Company, wa’adin makonni biyu ya gyara matsalar wuta da ake fuskanta a jihar ko kuma ya bar jihar.

Kakakin Majalisan Dokokin jihar Hon. Danladi Jatau tare da mambobinsa suka bayyana haka a ranar Talata, okacin tattaunawa da Shugabannin Kamfanin Abuja Electricity Distribution Company (AEDC) a zauren majalisar.

Kakakin majalisar, Hon. Danladi Jatau ne ya jagoranci zaman.

Bayan wakilan Kamfanin AEDC da NAEPA sun gurfana gaban majalisan.

Kakakin majalisar ya bukaci jagorarorin su bayyana a gaban mambobin matsalisar.

“sunana Injiniya Jonathan Adeyemi shugaban sashen kasuwanci da ke wakiltar Jihar Kogi, Neja da Jihar Nasarawa a kamfanin AEDC”.

Shi ma shugaban Nasarawa State Electricity Power Agency, (NAEPA ), Injiniya Suleiman Umar ya gabatar da kansa.

Majalisar ta gudanar da tambayoyi kan dalilin rashin samun wutan lantarki ga al’umman jihar masamman bangaren talakawan jihar.

Sannan ta bukaci da su bayyana mata adadin kwastomomin da ke amfani da lantarki a jihar.

Da adadin mita da ake amfani da kati da AEDC ta samar a fadin jihar.

Ta kuma bayyana kudin da ta samu daga watan daya zuwa watanni hudu na wannan shekarar.

Sannan ta bayyana yawan injinan rarraba wutar da ke unguwanni a fadin jihar.

Ta kuma bayyana karfin wutar da ta ke samarwa ga al’umman jihar.

Haka zalika ta bayyana dalilan da ya sa ba a samun isasshiyar wutar lantarki a Lafia, babban birnin jihar.

Majalisar ta bukaci shugaban samar da karfin hasken wutan lantarki ta jihar, Injiniya Sulaiman Umar, ya gaggauta kawo karshen aikin wutan lantarki a karamar hukumar Toto da yankin Umasha da kauyukan da ke kusa da yankin tun da Gwamna Abdullahi Sule ya mika makudan kudade domin samar da wutan lantarki.

‘Yan majalisar sun nuna rashin amincewarsu da tsarin da kamfanin AEDC ya ce yana yi na raba wutan lantarki kashi hudu.

Kamar yadda kamfanin ya bayyana cewa akwai sashen da ke samun wutar awa 20 da masu samun awa 16 da masu samun awa takwas da masu samun awa hudh.

Majalisar ta ce tun da kasuwanci suke yi kuma suna samun riba babu dalilin da zai bambamce masu amfanin da wutar.

Sannan majalisar ta gargadin kamfanin AEDC da cewa babu dalilin da idan injin wutan lantarki ko waya ta samu matsala a ce al’ummar unguwar ne za su hada kudi su gyara alhalin suna biyan kudin wuta.

Majalisar ta ce ba zai yiwu ba tun da al’umma na biyan kudin wuta bai kamata idan wuta ta samu matsala a ce su zasu gyara ba.

Duk da kokarin kare martabar kamfanoninsu, inda suka yi dogayen bayanai tare da amsa tambayoyi, kamfanin AEDC da NAEPA ba su gamsar da ‘yan majalisar ba.

Daga bisani majalisar ta ba su makonnj biyu da su gaggauta warware matsalar ko su sanya kafar wando daya da su.

People are also reading