Home Back

Waiwaye: Hukuncin kotu kan masarautun Kano da rikicin siyasar Rivers

bbc.com 2024/7/1

Wannan maƙala ce da ke kawo maku labaran muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya cikin makon jiya

Buhari ya nuna damuwa kan ƙaruwar yawan al’umma barkatai

Buhari

Asalin hoton, BUHARI SALLAU/X

A ranar Lahadin makon jiya, kuma ranar sallah ne tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi gargaɗin cewa yadda al'ummar ƙasar ke ƙaruwa cikin sauri ka iya zama matsala ga ƙasar matukar ba a ɗauki matakan da suka dace ba.

Yayin da yake jawabi wa manema labarai a Daura jim kaɗan bayan kammala Sallar Idi, tsohon shugaban ƙasar ya ce yawan ƙaruwar jama'a a ƙasar abin dubawa ne.

''Yadda al'umma ke ƙaruwa cikin sauri matuƙar ba a ɗauki mataki ba, zai kawo matsala ga al'umomi masu tasowa''.

“Don haka akwai buƙatar gangamin wayar da kan al'umma kan wannan matsala, tare da buƙatar zuba jari a ɓangarorin ilimi da na lafiya.”

'Yan bindiga sun sace mutane masu yawa a Sokoto

Ƴan bindiga

Asalin hoton, GETTY IMAGES

A cikin makon jiyan ne kuma wasu 'yan bindiga suka kai hari ƙauyen Tudun Doki da ke yankin ƙaramar hukumar Gwadabawa a jihar Sotoko inda suka kashe mutum biyar tare da sace mutanen da ba a san adadinsu ba.

Rahotonni sun ce 'yan bindigar sun far wa ƙauyen ne da tsakar daren ranar Sallah.

Gwamnatin Jihar ta tabbatar wa BBC faruwa kai harin, inda ta ce an jikkata fiye da mutum 30 a lokacin harin.

Jihar sokoto da ke arewacin ƙasar na daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro, inda 'yan bindiga ke sace mutane masu yawa a lokaci guda domin neman kuɗin fansa.

Hukuncin da kotu ta yanke game da shari'a kan sarautar Kano

Kano

Asalin hoton, MAI KATANGA/FACEBOOK

A ranar Alhamis ɗin makon jiya ne Babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar Kano a arewacin Najeriya ta ce dokar da ta rushe masarautu a jihar na nan daram amma kuma ta soke aiwatar da dokar wadda gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.

A lokacin yanke hukuncin, Mai Shari'a Abdullahi Muhammad Liman ya ce ba daidai bane gwamnan jihar Kano ya aiwatar da dokar soke masarautun saboda akwai umurnin kotun da aka bayar da ya dakatar da duk wani yunkuri na gwamnan Kano wajen aiwatar da sabuwar dokar da ta cire rawanin sarakuna biyar a jihar ta Kano.

Mai shari’a Liman ya ce “A don haka na bayar da umurnin cewa dukkan matakan da gwamnati ta ɗauka na soke su amma hakan bai shafi sabuwar dokar masarautu ba. Amma sun shafi matakan da gwamna ya dauka ciki har da sanya hannu a sabuwar doka da kuma sake nada Sanusi”.

Kotun ta ce “An soke dukkan matakan da masu kare kai a shari’ar suka ɗauka, amma kuma hakan bai shafi dokar ba.”

Gwamnan Rivers ya rantsar da shugabannin ƙananan hukumomi na riƙo

Rivers

Asalin hoton, RSG/FACEBOOK

A larabar makon jiyan kuma gwamnan Ribas Siminalayi Fubara ya rantsar da shugabannin riƙo na ƙananan hukumomin jihar 23

Gwamnan ya rantsar da shugabannin, bayan da da tun da farko majalisar dokokin jihar, ɓangaren da ke biyayya ga gwamnan ya tantance mutanen, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A ranar Litinin ne wa'adin mulkin tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomin waɗanda ke biyayya ga tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ƙare.

Ranar Talatar makon jiyan ne aka yi rikici a jihar bayan da Gwamna Fubara ya umarci shugabannin sassan mulki na ƙananan hukumomin su karɓi ragamar mulki, amma kuma aka samu hatsaniyar da ta yi sanadiyyar mutuwar mutum huɗu ciki har da ɗansanda ɗay da ɗansakai ɗaya.

Kwalara ta hallaka mutum 24 a Legas

Cholera

Asalin hoton, Reuters

A ranar juma'ar makon jiya aka fitar da bayanin barƙewar cutar kwalara a jihar Legas, inda aalkaluma suka nuna cewa cutar ta kashe mutum 24.

Rahoton da gwamnatin jihar ta Legas ta fitar, ya ce ana kuma zargin cewa mutum 417 sun kamu da cutar, inda aka tabbatar da 35 daga cikin kananan hukumomi 20 da ke faɗin jihar.

Mai bai wa gwamnan jihar shawara kan harkokin kiwon lafiya, Kemi Ogunyemi, ta ce alkaluman mutanen da suka mutu ya tashi daga 15 zuwa 21 a ranar Alhamis.

A cewarta, yankunan da aka fi samun masu kamuwa da cutar sun haɗa da Lagos Island, Kosofe, da kuma Eti Osa.

Ogunyemi da take bayar da ƙarin haske kan ɓarkewar cutar bayan zama da mambobin hukumar kiwon lafiya ta jihar, ta ce cutar ta ƙara yaɗuwa ne saboda taruwar jama'a da yawa a lokacin bukukuwan babbar sallah.

People are also reading