Home Back

Gwamnati ta Dage Zaman Mafi Karancin Albashi, Babu Ranar Cigaba da Tattaunawa

legit.ng 2024/7/2
  • Kwamitin gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago sun dage zaman da suke kan batun mafi karancin albashi har sai baba ta gani ba tare
  • Matakin na zuwa ne bayan an kasa cimma matsaya kan mafi karancin albashin da gwamnati ta ce N60,000 za ta iya biyan ma’aikatan duk da halin matsi d ake ciki
  • Amma kungiyar kwadago ta ce tana kan bakarta na bukatar gwamnati ta biya ma’aikatan kasar nan N497,000 a matsayin mafi karancin albashi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Kwamitin da ke tattaunawa kan mafi karancin albashi ya dage zaman tattaunawa har sai baba ta gani ba tare da bayyana dalilin hakan ba.

Kungiyar kwadago ta NLC ta ki amincewa da tayin gwamnati har sau uku na mafi karancin albashin domin a cewarta ya yi kadan.

Shugaban kasa
Gwamnati ta dage zama kan mafi karancin albashi a Najeriya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/@NLCHeadquarters Asali: Facebook

Punch News ta wallafa cewa kungiyar NLC da ta ‘yan kasuwa TUC na neman a biya N497,000 a matsayin mafi karancin albashi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta yi tayin mafi karancin albashi

Gwamnatin tarayya dai ta yiwa kungiyoyin kwadago tayin N60, 000 a matsayin mafi karancin albashi.

Nairaland ta wallafa cewa wannan kari ne kan tayin N57,000 da gwamnatin ta yi tun da fari, kuma tayi na biyu da ta yiwa kungiyar ta NLC.

Wata majiya ta tabbatar da cewa a zaman da aka sake yi tsakanin kungiyoyi da gwamnati, ba a samu damar cimma matsaya ba.

Hakan ta sa aka dage zaman ba tare da sake sanya ranar ci gaba da zaman ba.

Majiyar kungiyar NLC ta bayyana cewa za su sauko da bukatarsu daga N497,000 ne kawai idan gwamnati ta yi musu tayi mai gwabi.

NLC ta ki amincewa da albashin N60,000

A baya mun kawo muku labarin cewa kungiyar kwadago ta NLC da ta 'yan kasuwa (TUC) ta ki amincewa da sabon tayin mafi karancin albashi da gwamnati ta yi mata.

Gwamnatin ta yi karin ne daga tayin N57,000 da ta yiwa kungiyoyin tun da fari, lamarin da suke ganin ya yi kasa sosai idan aka kwatanta da bukatarsu ta a biya N497,000 ga ma'aikatan.

Asali: Legit.ng

People are also reading