Home Back

RA’AYIN PREMIUM TIMES: Darasin Kwamacalar Siyasar Ribas: Lokacin kawo ƙarshen siyasar ubangida ya yi

premiumtimesng.com 2 days ago
TURNUƘU DAGA RIBAS:. ‘Asibitoci biyu kaɗai ke aiki lokacin da na karɓi mulki a hannun Wike’ – Gwamna Fubara

Jihar Ribas ta afka cikin kwatagwangwamar ruɗanin siyasar mulkin jihar, tun cikin watan Oktoba, 2023. Wannan mumnunan yanayin da aka jefa jihar babbar barazana ce ga rayuka, musamman bisa la’akari ga yadda hakan ya haifar da rasa rayuka a wasu wuraren, lamarin da ya ƙara zubar da ƙima da darajar dimokraɗiyya.

Wannan kwatagwangwama dai ta ɓullo ne sanadiyyar saɓani da aka samu tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da tsohon ubangidan sa, kuma tsohon Gwamnan Ribas Nyesom Wike, ƙasa da watanni biyar bayan rantsar da Fubara a ranar 29 ga Mayu, 202$. Kamar dai dama hakan ake tafiya a jihar tun daga 2007 inda gwamnonin da ke barin gado ke amfani da maƙudan kuɗaɗen al’ummar jihar su ɗora wanda su ke so ya gaje su.

Babbar illar farko dai a irin wannan ita ce yadda ake ragargazar maƙudan kuɗaɗen jiha ana naɗa wanda gwamna ke so, ko ya cancanta ko bai cancanta ba.

Sai kuma barazana ta biyu ita ce gwamnan da ake yi wa ɗauki-ɗora ɗin sai ya zama boyi-boyin tsohon gwamnan da ya naɗa shi. Watau ya rasa ƙarfin ikon sa na gwamna mai cikakken iko, ya miƙa wuya ga ubangidan sa na siyasa, ya zama raƙumi-da-akala kenan. Domin wanda ya naɗa shi ne ke ce masa ga yadda zai tafiyar da mulkin jihar. To amma sau da yawa akan samu saɓani ya shiga tsakani har su rabu baram-baram.

Babu wanda ya san takamaimen babban abin da ya shiga tsakanin Gwamna Fubara da Wike, amma dai abin da kowa ya sani shi ne yadda saɓanin da ya shiga tsakanin su ya yi wa gwamnatin jihar mummunar illa.

A Jihar Ribas ‘yan Majalisar Dokoki 27 na goyon bayan Wike, yayin da sauran 3 daga cikin 4 masu goyon bayan Gwamna Fubara ke ta ƙoƙarin tsige waɗancan 27, tun cikin watan Oktoba. Su 3 ɗin kaɗai ne ke zaman majalisa, shi ma zaman a Gidan Gwamnatin Jihar Ribas su ke yi.

A kwamishinoni kuwa, 5 masu goyon bayan Wike sun sauka, daga baya suka koma, yayin da ‘yan majalisa 27 da aka zaɓa ƙarƙashin PDP suka koma APC. Ƙoƙarin sasantawar da Fadar Shugaban Ƙasa ta yi masu ta sa an ɗan yi tsit na ɗan taƙaitaccen lokaci, kafin daga baya lamarin ya ƙara dagulewa.

Wani dalilin rikici tsakanin gwamnan da Wike shi ne batun ci gaba da mulkin shugabannin ƙananan hukumomin waɗanda wa’adin mulkin su ya ƙare a ranar 17 ga Yuni, bayan sun shafe shekaru uku kan mulki. Sai ‘yan majalisa masu goyon bayan Wike su 27 suka ƙara masu watanni 6, shi kuma gwamna sai ya naɗa shugabannin riƙon ƙwarya, tunda wa’adin shugabannin ya cika. Kowanen su na tutiya da abin da Dokar Tsarin Mulki ta Kundin 1999, wadda aka yi wa kwaskwarima ta tanadar.

Rikicin siyasa yaro da ubangida irin ta Jihar Ribas, ba baƙuwa ba ce a dimokraɗiyyar mu. Mun ga irin haka a jihohin Anambra, Legas, Edo, Akwa Ibom, Abiya, Zamfara, Enugu, Kano, Sokoto, Delta da kuma abin da ya kunno kai yanzu a Jihar Kaduna.

To amma dai irin barazana da munin siyasar gwamna da ubangida wadda ta yi muni a Ribas, jiha mai albarkacin ɗanyen mai, babban dalili ne da zai sa a gaggauta kawo ƙarshen siyasar gwamna da ubangida, kafin ta haifar wa dimokraɗiyya mummunar illar da ba ta kankaruwa.

PREMIUM TIMES na mai ra’ayin cewa lokaci ya yi da za a samar da ƙwaƙƙwarar dokar da za ta yi wa shugaban ƙasa, gwamna ko ma wani dazagurun ɗan siyasa katanga, ta hana shi yi wa jam’iyya ƙarfa-ƙarfa ta hanyar naɗa wanda ya ga dama a takarar zaɓe, kamar dai yadda ake yi a Amurka.

Yin hakan zai ceci dimokraɗiyyar mu daga hannun masu nuna son ran su, ba son talakawan da aka ba su amanar shugabancin su ba.

People are also reading