Home Back

An Jikawa PDP Aiki, Kotu Ta Yi Hukunci Kan Zaben Fidda Gwani Ana Daf da Zabe

legit.ng 3 days ago
  • Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta rusa zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP da aka gudanar a jihar Edo
  • Kotun ta ce an saba dokokin kasa wurin gudanar da zaben wanda aka yi a watan Faburairun 2024 a jihar
  • Zaben da aka gudanar na PDP shi ya ba Asue Ighodalo nasarar zama sahihin dan takarar jam'iyyar a zaben da za a yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi hukunci kan sahihancin zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP a jihar Edo.

Kotun ta rusa zaben da aka gudanar a watan Faburairun 2024 wanda ya ba Asue Ighodalo nasarar zama dan takarar gwamna.

Kotu ta rusa zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP ana daf da zabe
Babbar Kotun Tarayya ta rusa zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP a jihar Edo. Hoto: Asue Ighodalo. Asali: Facebook

Hukuncin da kotun ta dauka kan PDP

Channels TV ta tattaro cewa Mai Shari'a, Inyag Ekwo shi ya yanke wannan hukunci inda ya ce ba a bi ka'idojin gudanar da zaben ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ekwo ya ce kwata-kwata ba a bi tsarin doka ba inda aka cire daliget 378 ba bisa ka'ida ba wurin gudanar da zaben fidda gwanin, cewar AIT News.

Kevin Mohammed shi ya shigar da korafin a madadin sauran daliget da abun ya faru da su a zaben domin kalubalnatar hakan.

Jigon PDP ya yi murabus a Edo

A wani labarin, kun ji cewa 'dan kwamitin yakin neman zaben gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Edo, Prince Felix Isuku, ya yi murabus daga muƙaminsa.

Babban jigon ya fice daga jam'iyyar PDP yayin da harkokin kamfe suka kankama ana daf da zaɓen gwamnan Edo wanda za a yi a watan Satumba 2024.

Prince Isuku ya bar PDP ne sa'o'i 48 bayan kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP ta jihar Edo ya kori tsohon mataimakin gwamna, Philip Shaibu.

Asali: Legit.ng

People are also reading